Bidiyon murnar da ta barke a Zaria bayan nada Bamalli a sabon Sarki

Bidiyon murnar da ta barke a Zaria bayan nada Bamalli a sabon Sarki

- Garin Zazzau ya dinke da shagali tare da murna bayan gwamnan jihar Kaduna ya bayyana sabon sarki

- Kamar yadda Gwamna Malam Nasir Ahmad El-Rufai ya bayyana, ya nada Alhaji Ahmad Bamalli domin zama sarkin Zazzau na 19

- Jama'a da dama sun dinga murna tare da yin cincirindo a fadar sarkin inda suka dinga kabbara bayan isowarsa

Murna da shagali ya barke a garin Zazzau bayan da gwamnan jihar Kaduna ya bayyana Alhaji Ahmad Bamalli a matsayin Sarkin Zazzau na 19.

Bayan bada sanarwar, garin ya dinke da farin ciki da murna tare da kabbarori.

Jama'a da dama sun dinga fatan alkhairi tare da taya sabon Sarkin Murna wannan karagar mai dumbin tarihi da ya haye.

Bidiyon murnar da ta barke a Zaria bayan nada Bamalli a sabon Sarki
Bidiyon murnar da ta barke a Zaria bayan nada Bamalli a sabon Sarki. Hoti daga @GovKaduna
Asali: Twitter

Idan za mu tuna, a a ranar 20 ga watan Satumban 2020 ne Allah ya yi wa balaraben Sarki, Alhaji Dakta Shehu Idirs rasuwa.

Ya rasu yana da shekaru 84 a duniya bayan kwashe shekaru 45 da yayi a karagar mulkin.

Jama'a da dama sun yi cincirindo a fadar sarkin inda suka jira isowarsa sannan suka raka sa har ciki.

KU KARANTA: Operation Kashe Mugu: NAF ta kaddamar da sabon shirin kawar da 'yan bindiga a Arewa

KU KARANTA: Iyalai 12,000 za su amfana da tallafin tsabar kudi a jihar Kano

A wani labari na daban, labari da duminsa da ke zuwa wa Legit.ng shine sanarwar gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufai na sabon Sarkin Zazzau.

Kamar yadda Gwamnan jihar Kaduna ya wallafa a shafinsa na Twitter, ya bayyana Ahmed Nuhu Bamalli a matsayin Sarkin Zazzau na 19.

Ya gaji marigayi mai martaba, Alhaji Dakta Shehu Idris wanda ya rasu a ranar Lahadi, 20 ga watan Satumban 2020 bayan kwashe shekaru 45 da yayi a karagar mulkin.

Kamar yadda takardar ta bayyana, "Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmed El-Rufai, ya amince da nadin Alhaji Ahmed Nuhu Bamalli a matsayin sarkin Zazzau na 19.

"Ya maye gurbin marigayi Alhaji Dakta Shehu Idris, wanda ya rasu a ranar Lahadi, 20 ga watan Satumban 2020 bayan kwashe shekaru 45 da yayi a kan karagar mulki.

"Alhaji Ahmed Bamalli shine Sarki na farko daga gidan Mallawa a cikin shekaru 100 tun bayan rasuwar kakansa, Sarki Dan Sidi a 1920."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel