Dalilin da ya sa ya zama wajibi APC ta ci zaben Bayelsa - Buni

Dalilin da ya sa ya zama wajibi APC ta ci zaben Bayelsa - Buni

- Jam'iyyar APC ta jaddada kudurin nan na yin duk mai yiyuwa don cin zaben maye gurbin kujerun 'yan majalisun dattijai na jihar Bayelsa

- Shugaban jam'iyyar, Mala Buni, ya bayyana hakan a yayin kaddamar da kwamitim mutum 11 da za su jagoranci yakin zaben jam'iyyar a Bayelsa

- Mala Buni ya ce, samun nasarar cin zaben ne kawai zai baiwa jam'iyyar APC tagomashi a shiyyar Kudu maso Kudu, inda ta ke da babban gibi

Jam'iyyar APC ta ce za ta tabbata ta samu nasarar lashe zaben kujerun 'yan majalisun dattijai a jihar Bayelsa, makonni bayan shan kasa a zaben Edo.

Shan kayi a hannun jam'iyyar PDP a zaben Edo, shi ne ya tabbatar da gibi ga shugabancin jihohin Kudu maso Kudu ga jam'iyyar ta APC.

Shugaban rikon jam'iyyar na kasa, Mala Buni, ya bayyana hakan a ranar Talata a Abuja, yayin kaddamar da kwamitin mutum 11 da zasu jagoranci jam'iyyar a zaben Bayelsa.

KARANTA WANNAN: Hotunan Buhari yana jagorantar zaman majalisar zartaswa na ranar Laraba

Dalilin da ya sa ya zama wajibi APC ta ci zaben Gwamnan Bayelsa - Buni
Dalilin da ya sa ya zama wajibi APC ta ci zaben Gwamnan Bayelsa - Buni - @PremiumTimesng
Asali: Twitter

Mr Buni, a jawabinsa, ya ce lashe zaben kujerun majalisar dattijan biyu, "zai taimaka wajen sake bamu karfi a Kudu maso Kudu, shiyyar da APC ba ta da wani gwamna mai ci."

"Samun nasarar wannan zaben na da muhimmanci saboda bamu damar samun karfi a majalisar tarayya don kara hadin kai da shugaban kasa Buhari wajen samar da dokokin ci gaban kasa.

"Ya zama wajibi garemu jam'iyya mai mulki a kasar, da mu tabbata mun ci gaba da mulki na tsawon wa'adi biyar ko sama da hakan, don tabbatar da ci gaban jam'iyyar da kasar baki daya."

KARANTA WANNAN: Boko Haram: Rundunar soji ta karbi sabbin tankokin yaki da sauran sabbin makamai na zamani

Za a gudanar da zaben maye gurbin ne bayan da dan takarar gwamnan jihar karkashin PDP, Duoye Diri da mataimakinsa, Lawrence Ewhrudjakpo suka yi murabus.

Diri da Ewhrudjakpo su ne 'yan majalisun dattijai na mazabar Bayelsa ta tsakiya da ta Yamma a majalisar tarayyar kasar ta tara.

A wani labarin, Ministan sadarwa da gina sabon tsarin tattalin arziki ta hanyar fasahar zamani, Dakta Isa Ali Pantami, ya yabawa kokarin shugaban kasa, Muhammadu Buhari.

A cewar ministan, shugaba Buhari ya taimaka matuka wajen saka Najeriya a sahun gaba a cikin kasashen nahiyar Afrika da duniya da su ke taka rawar gani a bangaren fasahar zamani.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel