Da duminsa: Buhari ya jagoranci zaman majalisar zartaswa a Abuja

Da duminsa: Buhari ya jagoranci zaman majalisar zartaswa a Abuja

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranci zaman majalisar zartaswar gwamnatin tarayya a dakin taro na fadar shugaban kasa da ke babban birnin tarayya Abuja.

Hadimin shugaban kasar ta fuskar gidajen Radio da Talabijin, Buhari Sallau ya wallafa sanarwar hakan a ranar Laraba 7 gan watan Oktoba, 2020.

Daga cikin mahalarta taron majalisar zartaswar a fadar shugaban kasar, akwai ministan sadarwa da bunkasa tattalin arziki na zamani, Dr. Isah Ali Pantami.

KARANTA WANNAN: Buhari ya amince a bawa daliban da suka yi karatun NCE aiki, ya kara shekarun aikin malamai

Da duminsa: Hotunan Buhari yana jagorantar zaman majalisar zartaswa na ranar Laraba
Hotunan Buhari yana jagorantar zaman majalisar zartaswa na ranar Laraba - @Buharisallau1
Asali: Twitter

Sauran wadanda su ke tare da shugaban kasar sun hada da mataimakinsa, Yemi Osinbanjo; Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha; da shugaban ma'aikatan Buhari, Ibrahim Gambari, da dai sauransu.

Wannan shine taron majalisar zartaswar na karshe, kafin Buhari ya gabatar da daftarin kasafin 2020 gaban majalisar dokokin tarayya.

An shirya gabatar da kasafin ne a ranar Alhamis mai zuwa.

Da duminsa: Hotunan Buhari yana jagorantar zaman majalisar zartaswa na ranar Laraba
Hotunan Buhari yana jagorantar zaman majalisar zartaswa na ranar Laraba - @Buharisallau1
Asali: Twitter

Da duminsa: Hotunan Buhari yana jagorantar zaman majalisar zartaswa na ranar Laraba
Hotunan Buhari yana jagorantar zaman majalisar zartaswa na ranar Laraba - @Buharisallau1
Asali: Twitter

Da duminsa: Hotunan Buhari yana jagorantar zaman majalisar zartaswa na ranar Laraba
Hotunan Buhari yana jagorantar zaman majalisar zartaswa na ranar Laraba - @Buharisallau1
Asali: Twitter

A wani labarin, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince a dauki daliban NCE aikin gwamnati kai tsaye da zaran sun kammala karatun su.

Ministan ilimi, Alhaji Adamu Adamu a ranar Litinin, 5 ga watan Oktoba ya bayyana hakan, a babban birnin tarayya Abuja, yayin bukin murnar zagayowar ranar malamai ta duniya.

Haka zalika, shugaban kasar ya amince da bayar da gurbin karatu na kai tsaye tare da daukar nauyin karatun 'ya'yan malamai.

KARANTA WANNAN: Za mu fara binciken karkatar da kudin ciyarwa N2.6bn - FG

Shugaban kasar, ya kuma bayar da umurni da a kara kudin albashin malaman makarantar tare da tsawaita shekarun aikin su.

Legit.ng Hausa ta ruwaito maku cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amice da karin albashi ga malaman makaranta, ya sanar da hakan a murnar ranar malamai ta duniya.

Shugaban kasar ya kara wa'adin shekarun aikin malaman daga 35 zuwa 40, yayin da ya ke albishir da kara albashin malaman don basu kwarin guiwar gudanar da ayyukansu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel