Operation Kashe Mugu: NAF ta kaddamar da sabon shirin kawar da 'yan bindiga a Arewa

Operation Kashe Mugu: NAF ta kaddamar da sabon shirin kawar da 'yan bindiga a Arewa

- Shugaban Hukumar sojojin sama, Air Marshal Sadique ya bayyanar da sabon shirin ragargazar 'yan ta'adda

- Ya ce Shirin zai tabbatar da cewa an gano duk wata maboyar 'yan bindiga a Najeriya kuma an ragargaje su

- Ya ce ta haka ne kadai za'a samu a magance matsalar ta'addanci a yankin arewa da Najeriya gaba daya

Hukumar sojin sama a ranar Talata, sun kaddamar da sabon shirin ragargazar maboyar 'yan bindiga don kawar da ta'addanci da rashin tsaro a kasar nan.

Sabon shirin ragargazar 'yan ta'addan yana daya daga cikin wani shiri na Operation Kashe Mugu 2.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa jiragen NAF, tare da jiragen Beechcraft KingAir, Agusta 109 power helicopter, Alfa jet da MI 35 da su aka kaddamar da shirin a NAF Kaduna.

Daily Trust ta ruwaito cewa, Alfa jets sun dawo bayan minti 15 da tashinsu zuwa ga Shugaban dakarun sama, Air Marshal Sadique Abubakar a filin daga.

Duk da dakarun sama ba za su sanar da wurin ragargazar ba, wakilinmu ya bayyana mana cewa Birnin Gwari da Kajuru na cikin wuraren da aka fi mayar da hankali.

CAS ya sanar da manema labarai cewa an samu nasarar shirin nan, kuma anyi hakan ne don kawar da ta'addanci a jihar.

Ya ce: "Dole yan bindigar za su bar wurin, za kuma mu tsananta tsaro don kare mutanenmu yadda babu dan ta'addan da zai samu maboya a daji.

"Zamu tabbatar da cewa idan sun fito, yan sanda sun tare garuruwa, mu kuma mu ragargaje su. Wadanda ke tunanin za su boye a daji sai mun tabbatar basu samu wurin buya ba.

"Wannan shine shiri na biyu da muka yi, kuma yanzu haka zamu kara yin wani. Zamu tabbatar an gano maboyar su, musamman na Kaduna da Zamfara sannan muyi raga-raga dasu."

Ya tabbatar da cewa za su yi kaca-kaca da maboyar 'yan ta'addan, don su tabbatar da Arewa, yamma, gabas da kudu duk sun samu cikakken tsaro, yadda gaba daya kasar zata gyaru.

KU KARANTA: Rikici kadan ke hada mu ta dinga zazzabga min mari - Magidanci ya sanar da kotu

Dakarun sojin sama sun ragargaji maboyar 'yan bindiga a arewacin Najeriya
Dakarun sojin sama sun ragargaji maboyar 'yan bindiga a arewacin Najeriya. Hoto daga Daily Trust
Asali: Facebook

KU KARANTA: Gwamnatin Zamfara ta samu kwangilar samar da gwal na N5bn - Matawalle

A wani labari na daban, an ceto ma'aikatan gwamnatin jihar Borno 5 da 'yan kungiyar ISWAP sukayi garkuwa dasu watan da ya gabata.

Anyi garkuwa da ma'aikatan RRR dinne, yayin da suke kan hanya tsakanin Maiduguri da Monguno.

Ma'aikatan 5 sun bayyana a wani bidiyo ne jiya suna neman taimakon gwamnatin jihar Borno. 'Yan ta'addan sun yi ikirarin kai wa ma'aikatan gwamnati farmaki akan aikin da suke yi wa "makiya addinin musulinci."

'Yan ta'addan sun yi ikirarin hakan kafin su kai wa ma'aikatan farmaki, inda suka kama wasu ma'aikatan tsaro a watan Ogusta.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Online view pixel