Wata mata ta yi alhinin mutuwar karenta tamkar mutum, ta rubuta ta'aziyya mai ratsa zuciya

Wata mata ta yi alhinin mutuwar karenta tamkar mutum, ta rubuta ta'aziyya mai ratsa zuciya

- Wata mata mai suna Sallie ta nuna tsananin kaunar da ta ke yi wa karenta

- Ta wallafa ta'aziyyarsa cike da damuwa da kalamai masu taba zuciya

- Ta ce yanzu haka tana cikin matsananciyar damuwa sakamakon rashinsa

Wata mata mai suna Sallie, ta nuna tsananin kaunar da take wa karenta, har tana rubuta ta'aziyya mai ratsa zuciya.

Matar 'yar asalin Carolina, ta wallafa ta'aziyyarta a kafar sada zumuntar zamani ta Instagram inda masoya karnuka suka yi ta mika sakonnin ta'aziyyarsu gareta.

Kamar yadda ta rubuta takardar ta'aziyyar, karenta mai suna Charlie ya mutu ranar Lahadi, 13 ga watan Oktoba 2020 yana da shekaru 7 da haihuwa, sakamakon mummunar cutar daji da yayi ta fama da ita.

A yadda ta wallafa, "Charlie na son rayuwa, yana son zama gefen ruwa, yawo a mota, cin ayaba da kuma saka safa, sai dai ya tsani hawa bene."

A yadda Sallie ta wallafa, "Zan yi kewar Charlie, da murmushinsa. Allah sarki Charlie, Kai ne mafi soyuwa a gareni, a tsawon shekaru 7 da muka yi tare, ka koya min abubuwa da dama na rayuwa, na tabbatar bazan taba samun kamar ka ba.

"Yanzu haka zuciyata ta karye, nasan cewa yanzu haka baka fama da wata cuta, amma ka barni da kewar ka.

"Na yi farin cikin kasancewa tare da kai, ina matukar sonka, yaron kirki."

Wata mata ta yi alhinin mutuwar karenta tamkar mutum, ta rubuta ta'aziyya mai ratsa zuciya
Wata mata ta yi alhinin mutuwar karenta tamkar mutum, ta rubuta ta'aziyya mai ratsa zuciya. Hoto daga Sallie Hammett
Asali: Instagram

KU KARANTA: Osinbajo ya kalubalanci tsarin da FG take bi wurin nade-nade

KU KARANTA: Buhari ya bukaci taimakon 'yan majalisa wurin tsamo mutum 10m daga talauci

A wani labari na daban, hakika duk uwa tagari tana wahala wurin taso da ya'yanta tun yarinta har girmansu. Sai dai ace Allah ne zaiyi sakayya kawai. Bidiyon wata mata mai sana'ar fenti, mai suna Sognan Silla ya karade kafafen sada zumuntar zamani, inda aka ga matar tana sana'arta goye da jaririnta.

A bidiyon, matar na tsaye akan wani benci tana shafawa silin din wani daki fenti. Hakika bidiyon ya karade kafar sada zumuntar zamani ta Facebook, wanda fiye da mutane 400,000 suka gani.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel