Gwamnatin Zamfara ta samu kwangilar samar da gwal na N5bn - Matawalle

Gwamnatin Zamfara ta samu kwangilar samar da gwal na N5bn - Matawalle

- Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle ya shirya tsaf wurin fara sayar wa kasashen waje zinaren da aka hako a jiharsa

- Matawalle ya ce dama can suna da yarjejeniya da wasu kasashe akan siyar musu da danyen zinare mai kimar Naira biliyan 5

- Yace wannan turbar ita ce zata bai wa 'yan jiharsa damar morewa daga kudaden ma'adanai kuma jihar zata samu cigaba mai tarin yawa

Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara ya bayyana yadda gwamnatinsa ta tanadi zinari mai kimar Naira Biliyan 5 ga abokan kasuwancinsu na kasar waje.

Zailani Bappa, mai bai wa gwamnan shawara akan yada labarai, ya bayyana hakan ga manema labarai a wata takarda a Gusau, babban birnin jihar.

Matawalle ya bayyana yadda dama yake da yarjejeniyar sayar wa wasu abokan kasuwancinsu dunkulen zinare na Naira biliyan 5 da dadewa.

Matawalle ya sanar da yadda yanzu haka suka siya kilograms 31 na zinare a wurin masu hako zinare daga kasa a jihar.

A cewarsa, wannan dama ce da zasu bunkasa kudin shigar jihar Zamfara.

KU KARANTA: Da duminsa: Buhari ya amince da fitar da biliyan 10 domin kidaya

Gwamnatin Zamfara ta samu kwangilar samar da gwal na N5bn - Matawalle
Gwamnatin Zamfara ta samu kwangilar samar da gwal na N5bn - Matawalle. Hoto daga @Dailynigerian
Asali: Twitter

KU KARANTA: Bayan kashe 7m a shirin biki, ango ya fasa a ranar aure, ya bayyana dalilinsa

"Muna samun danyen zinaren ne a hannun masu hako zinare daga kasa. Muna wannan kokarin ne don tabbatar da cewa 'yan jihar Zamfara sun amfana da ma'adanan jihar," a cewarsa.

Gwamnan ya ce jihar zata cigaba da adana zinaren a bankuna, kuma ya tabbatar da cewa ba zai rintsa ba har sai jihar Zamfara ta bunkasa kuma ta kara kima a idon duniya.

Ya kara da cewa, "Matsalar da ake samu ita ce yadda idan masu hako zinare sun hako kuma sun fitar dashi kasar waje ba tare da wasu 'yan jihar sun amfana ba. Wannan mukeso mu gyara."

A wani labari na daban, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi kira ga majalisar tarayyar kasar nan da ta tallafa wa mulkinsa wurin tsamo mutum miliyan 100 a fadin kasar nan.

Shugaban kasar ya yi wannan kira ne a ranar Litinin, 5 ga watan Oktoba yayin taron majalisar zartarwa da majalisar tarayya wanda aka yi a dakin taron gidan gwamnati da ke Abuja.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel