Buhari ya bukaci taimakon 'yan majalisa wurin tsamo mutum 10m daga talauci

Buhari ya bukaci taimakon 'yan majalisa wurin tsamo mutum 10m daga talauci

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi kira a kan hadin kai daga 'yan majalisu wurin tabbatar da cigaba

- Shugaban kasar ya yi kira ga 'yan majalisun wurin tabbatar da tsamo 'yan Najeriya miliyan 100 daga talauci

- Buhari ya kara da bayyana wasu abubuwan cigaba tara da mulkinsa zai sa gaba domin tabbatar da cigaba ga 'yan Najeriya

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi kira ga majalisar tarayyar kasar nan da ta tallafa wa mulkinsa wurin tsamo mutum miliyan 100 a fadin kasar nan.

Shugaban kasar ya yi wannan kira ne a ranar Litinin, 5 ga watan Oktoba yayin taron majalisar zartarwa da majalisar tarayya wanda aka yi a dakin taron gidan gwamnati da ke Abuja.

Kamar yadda takardar da mai magana da yawun shugaban kasa, Femi Adesina ya fitar, shugaban kasar ya jaddada bukatar alaka mai karfi tsakanin 'yan majalisar da fannin shari'a domin gaggauta kawo cigaba.

Shugaban kasar ya kara da cewa, ya bayyana wasu fannoni tara da mulkinsa zai mayar da hankali a cikin shekaru uku da suka rage masa domin tabbatuwar cigaba ga 'yan Najeriya.

KU KARANTA: Bidiyon matar aure dauke da goyo tana fenti don samun abun ciyar da 'ya'yanta

Buhari ya bukaci taimakon 'yan majalisa wurin tsamo mutum 10m daga talauci
Buhari ya bukaci taimakon 'yan majalisa wurin tsamo mutum 10m daga talauci. Hoto daga Femi Adesina
Asali: Twitter

KU KARANTA: Bayan kashe 7m a shirin biki, ango ya fasa a ranar aure, ya bayyana dalilinsa

A wani labari na daban, gwamnatin tarayya tayi ala-wadai akan 'yan Najeriyan dake cewa Najeriya na gab da tarwatsewa.

Garba Shehu, mai magana da yawun shugaban kasa ya fadi hakanne a wata takarda ta ranar Lahadi, 14 ga watan Oktoba wanda yake cewa rashin kishin kasa ne furta wadannan kalamai.

Gwamnatin tarayya ta zargi wasu 'yan Najeriya akan maganganun nuna rashin kishin kasa. Garba Shehu ya ce gwamnatin Buhari ba za ta lamunci irin wadannan kalubalan ba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel