Babbar magana: Jerin mutane 350 da suka mutu amma har yanzu ana biyansu albashi a Niger

Babbar magana: Jerin mutane 350 da suka mutu amma har yanzu ana biyansu albashi a Niger

- Gwamnatin jihar Niger ta gano mutane 340 da suka riga suka mutu amma har yanzu ana biyansu albashi

- Haka zalika, gwamnatin ta gano mutane 3,000 da suka kama aiki ta hanyar amfani da takardun bogi

- Ma'aikata 169 ne aka gano babu sunayensu a jadawalin ma'aikatan da za a biya albashi na watan Satumbar 2020 a jihar

Wani bincike na gwamnatin jihar Niger ya gano ma'aikata 340 a jihar da suka riga suka mutu ko suka yi ritaya amma har yanzu ana biyansu albashin cikakkun ma'aikata.

Haka zalika, gwamnatin ta gano ma'aikata 3,000 da suka kama aiki ta hanyar amfani da takardun bogi.

Wani kwamiti da gwamnatin jihar ta kafa ya yi binciken kwakwaf kan kudaden da jihar ke kashewa wajen biyan albashi, an samar da rahoton binciken ga manema labarai a Minna.

KARANTA WANNAN: Rundunar yan sanda ta samar da lambobin kira idan jami'anta sun ci zarafin ka

Babbar magana: Jerin mutane 350 da suka mutu amma har yanzu ana biyansu albashi a Niger
Babbar magana: Jerin mutane 350 da suka mutu amma har yanzu ana biyansu albashi a Niger - @channelstv
Asali: UGC

Shugaban kwamitin kuma kwamishinan ma'aikata, Ibrahim Panti ya shaidawa manema labarai cewa an gudanar da binciken bayan da shugaban ma'aikatan jihar ya gabatar da sunayen ma'aikata 26,387 don tantance su.

Sai dai a cewar sa, kwamitin ya gano cewa, ma'aikata 25,861 ne kawai suka yiwa kawunansu rejista a shafin tantance ma'aikatan a yanar gizo.

Panti ya kuma bayyana cewa ma'aikata 1,789 ba su kammala tantancewa ba saboda matsalar takardu, yayin da ma'aikata 773 suka ki kai kansu don a tantance su.

KARANTA WANNAN: Gwamnoni sun aike da muhimmin sako ga 'yan Nigeria

Ma'aikata 169 ne aka gano babu sunayensu a jadawalin ma'aikatan da za a biya albashi na watan Satumbar 2020 daga ofishin shugaban ma'aikatan.

Kwamitin ya ce har yanzu yana nazari kan matsalolin da wasu ma'aikata suka samu, sannan za su saurari ma'aikatan da ke da kwararan hujjojin rashin zuwa tantancewar ne kawai.

Panti ya kara da cewa takardu da bayanan da aka yi amfani da su wajen tantancewar na nan, don amfanin mutane da kuma masu ruwa da tsaki na gwamnati.

A wani labarin, Sunday Dare, ministan matasa da bunkasa wasanni, ya ce gwamnatin tarayya karkashin shugaban kasa Muhammadu Buhari na shirin daukar matasa miliyan daya aiki.

Dare ya bayyana hakan ne a ranar Juma'ar makon da ya gabata, a yayin wani bukin baje kolin kasuwanci na fasahar matasa a babban birnin tarayya Abuja.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Online view pixel