Babban ci baya ne gareni idan aka bukaci in zama shugaban kasa - Bishop Oyedepo

Babban ci baya ne gareni idan aka bukaci in zama shugaban kasa - Bishop Oyedepo

- David Oyedepo, fasto shugaban Living Faith Church Worldwide yace ci baya ne zama shugaban kasa a gareshi

- Yace a matsayin da ya taka yanzu haka, duk wanda yace yayi takarar Shugaban kasa ya kaskantar dashi

- Yace a yanzu haka, kasashe fiye da 100 suna neman fatawa da kuma taimakonsa, don haka ba zai so ya jagoranci kasa daya tak ba

David Oyedepo, faston daya kirkiro Living Faith Church Worldwide wadda aka fi sani da Winners Chapel yace idan aka ce yayi takarar shugaban kasa an mayar dashi baya.

A cewar shi, Ubangiji ya tambayeshi idan yana so ya kai kololuwa a shekarar 1984, duk da daraja ce mutum ya zama shugaban kasa, amma gaskiya ba shi da wannan ra'ayin.

Ya ce a ranar Lahadi, 4 ga watan Oktoba, "duk abinda nace kuyi, kuyi. Kada ma ku tsaya wani tunani: duk abinda nace ku aikata, ku aikata.

"Kada ku kuskura ku yi wani dogon nazari akai: ko menene nace kuyi, to kuyi. Kada ku kuskura kuyi abinda kuka ga suna yi: kawai kuyi abinda na saka ku.

"Dalilin da yasa nace muku ci baya ne zamana shugaban kasa kenan...ina kara maimaitawa ne, akwai wadanda zasu yi ta maganganu amma ko a jikina."

"Ci baya ne a gareni idan aka ce in zama shugaban kasa a kasar nan. Duk da babbar daukaka ne zama shugaban kasa, amma hakan baya cikin tsari na. Matsayi na ya wuce nan, a cewar sa.

"Kasashe fiye da 100 suna neman taimakona, don haka daraja ta ta wuce zama shugaban kasa,"a cewar sa.

KU KARANTA: Ina alfahari da ayyukan cigaban da muka yi wa Najeriya tare da Obasanjo - Atiku

Babban ci baya ne gareni idan aka bukaci in zama shugaban kasa - Bishop Oyedepo
Babban ci baya ne gareni idan aka bukaci in zama shugaban kasa - Bishop Oyedepo. Hoto daga @Lindaikeji
Asali: Twitter

KU KARANTA: Sarkin Musulmi ya yi muhimmin kira ga shugabanni

A wani labari na daban, hakika duk uwa tagari tana wahala wurin taso da ya'yanta tun yarinta har girmansu. Sai dai ace Allah ne zaiyi sakayya kawai.

Bidiyon wata mata mai sana'ar fenti, mai suna Sognan Silla ya karade kafafen sada zumuntar zamani, inda aka ga matar tana sana'arta goye da jaririnta.

bidiyon, matar na tsaye akan wani benci tana shafawa silin din wani daki fenti. Hakika bidiyon ya karade kafar sada zumuntar zamani ta Facebook, wanda fiye da mutane 400,000 suka gani.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel