Da duminsa: Buhari ya amince da fitar da biliyan 10 domin kidaya

Da duminsa: Buhari ya amince da fitar da biliyan 10 domin kidaya

- Gwamnatin tarayya ta fara shiye-shiryen sake wata kidayar a shekarar 2021

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da bayar da biliyan 10 ga hukumar kidaya ta kasa

- Ya amince da bayar da kudin don bin lungu da sakon Najeriya don aiwatar da kidayar

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da bayar da Naira biliyan 10 ga hukumar kidaya ta kasa.

A yadda jaridar The Nation ta ruwaito, za'ayi amfani da kudin ne don bin lungu da sakon kananan hukumomi 774 dake kasar nan.

Jaridar Legit.ng ta tattaro bayanai akan yadda Shugaban kasa ya amince da karin Naira biliyan 4.5 akan kasafin 2021 don aiwatar da kidayar.

Osinbajo yayi magana akan yadda gwamnatin Buhari ya amince da bayar da Naira biliyan 10 domin kidayar.

Shugaban hukumar kidaya ta kasa, Eyitayo Oyetunji, ya bayyana hakan a Abuja ranar Litinin.

KU KARANTA: Ina alfahari da ayyukan cigaban da muka yi wa Najeriya tare da Obasanjo - Atiku

Da duminsa: Buhari ya amince da fitar da biliyan 10 domin kidaya
Da duminsa: Buhari ya amince da fitar da biliyan 10 domin kidaya. Hoto daga Femi Adesina
Asali: Facebook

KU KARANTA: Sarkin Musulmi ya yi muhimmin kira ga shugabanni

A wani labari na daban, gwamnatin tarayya tayi ala-wadai akan 'yan Najeriyan dake cewa Najeriya na gab da tarwatsewa.

Garba Shehu, mai magana da yawun shugaban kasa ya fadi hakanne a wata takarda ta ranar Lahadi, 14 ga watan Oktoba wanda yake cewa rashin kishin kasa ne furta wadannan kalamai.

Gwamnatin tarayya ta zargi wasu 'yan Najeriya akan maganganun nuna rashin kishin kasa. Garba Shehu ya ce gwamnatin Buhari ba za ta lamunci irin wadannan kalubalan ba.

Gwamnati zata tsaya tsayin-daka wurin kawar da duk wani abu da zai tada tarzoma da kuma hankulan 'yan kasa.

Ya ce gwamnati zata dage wurin kawar da matsalolin rashin tsaro da kuma cutar COVID-19.

Mai magana da yawun shugaban kasan, yace gwamnatin tarayya ba za ta dauki wani matakin da zai cutar da 'yan Najeriya miliyan 200 ba, wanda hakan ne abu na farko da Shugaban kasa ya dace yayi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel