Sunday Dare: Sabon shirin gwamnatin Buhari na samawa matasa 1,000,000 aiki a Nigeria

Sunday Dare: Sabon shirin gwamnatin Buhari na samawa matasa 1,000,000 aiki a Nigeria

- Gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta shirya daukar matasa 1,000,000 aiki kafin zuwan karshen watan Oktoba

- Ministan matasa da bunkasa wasanni, Sunday Dare ya bayyana hakan a Abuja, yana mai cewa, tuni Buhari ya amince a fitar da kudaden shirin

- Dare ya yi kira ga matasa da su tsumayi fitowar shirin, sannan su cike takardun da ake bukata, don su amfana da shirin

Sunday Dare, ministan matasa da bunkasa wasanni, ya ce gwamnatin tarayya karkashin shugaban kasa Muhammadu Buhari na shirin daukar matasa miliyan daya aiki.

Dare ya bayyana hakan ne a ranar Juma'ar makon da ya gabata, a yayin wani bukin baje kolin kasuwanci na fasahar matasa a babban birnin tarayya Abuja.

Ma'aikatar matasa da bunkasa wasanni tare da hadin guiwar gidauniyar 'I Choose Life' (na zabi rayuwa) suka shirya taron.

KARANTA WANNAN: Dalilin da ya sa gwamnatin Buhari ta cancanci yabo daga yan Nigeria - Malami

Sunday Dare: Sabon shirin gwamnatin Buhari na samawa matasa 1,000,000 aiki a Nigeria
Sunday Dare: Sabon shirin gwamnatin Buhari na samawa matasa 1,000,000 aiki a Nigeria - @thecableng
Asali: Twitter

An shirya taron ne domin bukin murnar cikar Nigeria shekaru 60 da samun 'yanci, da kuma taya matasa murna kan nasarar da suka samu a kasuwanci, kirkira, aikin hannu da fasahar zamani.

Taken taron shi ne, 'Mafarkin kasata Nigeria,' kamar yadda jaridar The Cable ta ruwaito.

A cewar Dare, ma'aikata matasa da bunkasa wasanni na hada karfi da karfe da sauran ma'aikatu don samar da ayyukan yi, lamarin da zai tabbata kafin karshen watan Oktoba, a cewar sa.

KARANTA WANNAN: Gwamnoni sun aike da muhimmin sako ga 'yan Nigeria

"Ma'aikatar matasa da bunkasa wasanni, ma'aikatar mata, sadarwa da tattalin arziki na zamani, kwadago da daukar ayyuka da sauran ma'aikatu, ke kokarin cimma wannan kudiri," a cewar sa.

"Tuni aka tattara tsarin aikin, kuma an samar da kudaden yin hakan. Ina baku tabbacin cewa kafin nan da karshen oktoba, shirin daukar matasan zai fara aiki a fadin kasar.

"Ina amfani da wannan damar wajen yin kira ga matasa da su zauna dakon kaddamar da wannan shiri, sannan su cike takardun da ake bukata, don su amfana da shirin."

Chijoke Obioma, shugaban gidauniyar 'Na zabi rayuwa', ya ce an shirya wannan taro "domin murnar cikar Nigeria shekaru 60 da samun 'yanci."

Ya kara da cewa gidauniyar za ta ci gaba da bayar da gudunmowa wajen ci gaban matasan Nigeria ta hanyar shirye shirye da kuma bayar da horo.

A wani labarin, Ministan Shari'a kuma Antoni Janar na kasa, Abubakar Malami ya ce gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta yi aikin azo a gani, bai kamata a zage ta ba, in har ba za a yaba mata ba.

Ya ce ya kamata mambobin jam'iyya mai mulki a kasar, su yi tunkaho da alfahari da gwamnati mai ci, la'akari da ayyukan raya kasa da ta shimfida a cikin yan shekarun nan.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel