Bidiyon matar aure dauke da goyo tana fenti don samun abun ciyar da 'ya'yanta

Bidiyon matar aure dauke da goyo tana fenti don samun abun ciyar da 'ya'yanta

- Wata mata, Sognan Silla ta dauki bidiyon kanta tana aiki da jaririnta a bayanta

- Matar wadda sana'arta fenti ne, tace ta dauki bidiyon ne da jaririnta a bayanta ba don tana aiki a haka ba

- Bidiyon ya karade Facebook, inda fiye da mutane 400,000 suka gani, suka yaba mata

Hakika duk uwa tagari tana wahala wurin taso da ya'yanta tun yarinta har girmansu. Sai dai ace Allah ne zaiyi sakayya kawai.

Bidiyon wata mata mai sana'ar fenti, mai suna Sognan Silla ya karade kafafen sada zumuntar zamani, inda aka ga matar tana sana'arta goye da jaririnta.

A bidiyon, matar na tsaye akan wani benci tana shafawa silin din wani daki fenti.

Hakika bidiyon ya karade kafar sada zumuntar zamani ta Facebook, wanda fiye da mutane 400,000 suka gani.

Ta wallafa bidiyon inda har tayi wani dan tsokaci akai, ta kuranta kanta, tace hakika abubuwan arziki basu biyo mutum, sai ya mike, ya dage kuma ya zage wurin nema da kansa.

Yayin da mutane da dama suka yi ta yaba mata akan namijin kokarin da tayi, wasu kuma sun ce tasa rayuwar jaririnta a cikin hatsari.

Ta mayar da martanin masu cewa tasa rayuwar jaririnta a hatsari, inda ta ce ta goya jaririnta ne yayin da zata dauki hoton don nuna wa duniya irin jajircewarta a matsayinta na uwa.

A tsokacin da tayi tace, "hakika duk wata nasara bata biyo mutum inda yake, sai ya fita ya nema.

Dangane da jaririna, kada ku damu, nayi bidiyonne don in nuna muku ni uwa ce. Ban taba aiki da jaririna a baya na ba.

KU KARANTA: Sanata Goje ya angwance da hamshakiyar GMD ta kamfanin Binani, Hajiya Aminatu (Hotuna)

Bidiyon matar aure dauke da goyo tana fenti don samun abun ciyar da 'ya'yanta
Bidiyon matar aure dauke da goyo tana fenti don samun abun ciyar da 'ya'yanta. Hoto daga Sogna Silla
Asali: Facebook

KU KARANTA: Ina alfahari da ayyukan cigaban da muka yi wa Najeriya tare da Obasanjo - Atiku

A wani labari na daban, wata budurwa mai suna Oluwafunlola, ta wallafa a kafar sada zumuntar zamani ta Twitter, yadda saurayinta ya yaudare ta.

Budurwar ta bada labarin yadda ta gano cewa saurayin da ta ke kauna yana da wata budurwa daban.

Ba wannan kadai ne yafi daga mata hankali ba, hankalinta ya tashi ne a lokacin da ta gano ashe amfaninta daya ne a wurin sa, wato girki. Kuma ko girkin, ba shi kadai ne take yi wa ba, har da dayar budurwarsa.

A yadda budurwar ta bada labari, tana tura wa saurayin nata abinci ne ta masu babur din haya. Idan dayar budurwar ta tambayi saurayin, sai ya ce ai dama aikawa yake yi ana siya mishi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel