Da zafinsa: An yi bata kashi tsakanin 'yan sanda da 'yan fashi, mutane 5 sun mutu

Da zafinsa: An yi bata kashi tsakanin 'yan sanda da 'yan fashi, mutane 5 sun mutu

- Rundunar 'yan sanda ta ce ta samu nasarar kashe wasu gagararrun yan fashi da makami guda biyar a jihar Akwa Ibom

- Yan fashin, a cewar rundunar yan sandan, sun kware a satar mota da sayarwa a jihohin Akwa Ibom da Cross Rivers

- C.P Ameingheme Andrew ya gargadi yan kungiyar asiri, fashi da makami, fyade da sauran miyagun laifuka, da su gaggauta kauracewa jihar

Rundunar 'yan sanda ta jihar Akwa Ibom ta ce ta samu nasarar kashe yan fashi da makami shida wadanda suka kware a satar mota da sayarwa a jihohin Akwa Ibom da Cross Rivers.

Kwamishin 'yan sanda na jihar, Mr. Ameingheme Andrew a ranar Juma'a a Uyo, yayin holen gawar 'yan fashin ya ce an kashe su ne yayin bata kashi a kan hanyar Calabar zuwa Itu.

Ya bayyana cewa yan fashin suna kan hanyar su ta zuwa sayar da wata motar sata kirar Toyota Camry da suka sata a hannun wani likita da ke zama a Calabar, inda dubunsu ta cika.

KARANTA WANNAN: Dalilin da ya sa na zabi bugawa Barcelona wasa akan Bayern Munich - Sergino Dest

Da zafinsa: An yi bata kashi tsakanin 'yan sanda da 'yan fashi, mutane 5 sun mutu
Da zafinsa: An yi bata kashi tsakanin 'yan sanda da 'yan fashi, mutane 5 sun mutu
Source: UGC

Kwamishinan wanda ya kama aiki kwanaki kadan da suka wuce, ya ce matattun yan fashin har sun tuntubi wanda za su sayarwa motar satar.

Ya kara bayyana cewa rundunar 'yan sandan ta afke wani kasurgumin mai yiwa mata fyade, ta kuma cafke wani da ake zargin sa da kisan kan wani yaro mai shekaru 11.

KARANTA WANNAN: Nigeria @60: Gwamnoni sun aike da muhimmin sako ga 'yan Nigeria

Haka zalika rundunar ta samu nasarar cafke 'yan kungiyar asiri guda biyar, da kuma wasu yan fashi da makami guda shida.

"A yau, da misalin karfe 5:30 na safiya, mun samu kwakkwaran rahoto akan wasu yan fashi da makami guda shida, akan hanyarsu ta sayar da motar sata.

"Da ma sun dade da addabar jihohin Akwa Ibom da Cross River, amma cikin nasara, bayan musayar wuta da jami'an rundunarmu, mun kashe su a hanyar Calabar zuwa Itu."

Kwamishinan ya gargadi yan ta'adda da ke a cikin kungiyar asiri, fashi da makami, fyade da sauran miyagun laifuka, da su kauracewa jihar, ko su dandani kudarsu a hannunsa.

Ya yabawa gwamnatin jihar da kuma al'umar Akwa Ibom akan goyon bayan da suka baiwa rundunar 'yan sanda a kokarinta na aiwatar da ayyukan da suka rataya a wuyanta.

Dr. Arinze Obinna, mamallakin motar da yan fashin ke shirin sayarwa, ya ce sun tsare shi da bindiga yayin da ya ke kan hanyar komawa gida, inda suka kwace motar.

A wani labarin, Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni ya ba da tabbacin cewa Boko Haram ta kusa zama tarihi a mulkin Buhari, kasancewar yan ta'adda ba za su iya fin karfin shugabanni da mabiyansu ba.

Buni ya bayyana hakan ne a ranar Talata a Maiduguri yayin jajantawa Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno, kan harin da Boko Haram ta kai wa tawagarsa a hanyar zuwa Baga.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel