Dalilin da ya sa na zabi bugawa Barcelona wasa akan Bayern Munich - Sergino Dest

Dalilin da ya sa na zabi bugawa Barcelona wasa akan Bayern Munich - Sergino Dest

- Tsohon mai takewa Ajax baya, Sergino Dest ya warware zare da abawa, kan dalilin da ya sa ya zabi buga wasa a Barcelona mai makon kungiyar Bayern Munich

- Sergion Dest, ya ce tuni ya kammala shirye shiryen komawa Bayern Munich, amma makonni biyu da suka wuce, Barcelona ta fara zawarcin sa

- A cewarsa, buga wasa a Barca, tamkar mafarki ne ya zama gaskiya a gare shi

Tsohon mai takewa Ajax baya, Sergino Dest ya bayyana dalilin da ya sa ya fifita Barcelona akan zakarun kofin nahiyar turai, Bayern Munich.

Tsohon dan wasan na Ajax, ya zabi bugawa Barca wasa, akan kudi €21m.

"Duk wani yanayi da nake samu abun alfahari ne," a cewar Dest. "Abun tunkaho ne in buga wasa a kungiyar kwallon kafa da ta kafa tarihi a duniya, kuma mafarkina ya zama gaskiya"

KARANTA WANNAN: Nigeria @60: Gwamnoni sun aike da muhimmin sako ga 'yan Nigeria

Dalilin da ya sa na zabi bugawa Barcelona wasa akan Bayern Munich - Sergino Dest
Dalilin da ya sa na zabi bugawa Barcelona wasa akan Bayern Munich - Sergino Dest - @FCBarcelona
Source: Twitter

"Na zo ne domin in buga wasa da kungiyoyin da suka zarce sa'a a duniya. Matakin farko da na ke so shine samun ci gaba, buga wasa mai kyau da kuma samun nasara a kowanne lokaci."

Dest ya bayyana cewa yana dab da zabar Bayern Munich kafin kungiyar Barca ta kawo masa hari.

"Har sai makonni biyu da suka gabata, ina shirin zuwa kungiyar Bayern Munich. Amma, Bayern ba ta sa kudi masu yawa ba, kuma Barca ta gabatar da tata bukatar. Komai daga nan ya canja.

KARANTA WANNAN: Buhari ya yi amai ya lashe ana gobe bikin Nigeria @60

"Na canja ra'ayina kuma na yi nazari kan nazari na tsawon lokaci, kafin na zabi kungiyar Barca."

Ya kara da cewa: "Zuwana wannan babbar kungiyar kwallon kafar a wannan kaka, zan iya cewa, mafarkina ya zama gaskiya."

A wani labarin, Ministan Shari'a kuma Antoni Janar na kasa, Abubakar Malami ya ce gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta yi aikin azo a gani, bai kamata a zage ta ba, in har ba za a yaba mata ba.

Ya ce ya kamata mambobin jam'iyya mai mulki a kasar, su yi tunkaho da alfahari da gwamnati mai ci, la'akari da ayyukan raya kasa da ta shimfida a cikin yan shekarun nan.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel