2023: An bayyana Tinubu a matsayin wanda zai gaji Shugaba Buhari

2023: An bayyana Tinubu a matsayin wanda zai gaji Shugaba Buhari

- Wasu matasa sun fito sun bayyana yadda zasu mara wa Bola Tinuba baya, don ganin ya zama shugaban kasar Najeriya

- Matasan suna so Tinubu ya tsaya a matsayin dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar APC a zaben 2023

- Ahmed Ibrahim, shugaban kungiyar yana rokon 'yan Najeriya su mara wa Tinubu baya don yaci zaben 2023

Wata kungiyar matasa 'yan jam'iyyar APC, sun zabi Bola Tinubu a matsayin shugaban da zai maye gurbin shugaban kasa Muhammadu Buhari a shekarar 2023.

Kungiyar matasan sun bayyana yadda yanzu haka suke fadi-tashin ganin sun ga lallai Tinubu ne zai tsaya a matsayin dan takarar shugabancin kasa a jam'iyyar APC a shekarar 2023.

Jaridar This Day ta bayyana yadda matasan suke kokarin ganin Tinubu ya maye gurbin shugaba Muhammadu Buhari idan wa'adin mulkinsa ya cika a shekarar 2023.

Shugaban kungiyar UGC na kasa, Ahmed Muhammad Ibrahim, ya ce sun yanke shawarar tsayar da Tinubu a matsayin dan takarar shugaban kasa saboda yanayin tsarin mulkinsa na musamman ne.

KU KARANTA: Yadda bakanike ya tsere da motar kwastoma daga kai masa gyara

Shugaban kungiyar ya ce: "Tinubu dai ikon Allah ne, kuma yana da farin jini a duk fadin kasar nan. Yana da halayen shugabanni.

"Tinubu yana da fasaha da kuma iko ta yadda zai iya dorawa daga inda Buhari zai tsaya."

Ibrahim ya roki 'yan Najeriya su taimaka su bada hadin kai don ganin Tinubu ya zama shugaban kasa a shekarar 2023.

2023: An bayyana Tinubu a matsayin wanda zai gaji Shugaba Buhari
2023: An bayyana Tinubu a matsayin wanda zai gaji Shugaba Buhari. Hoto daga The Nation
Source: UGC

KU KARANTA: Gwamnoni sun kai wa Zulum ziyara, sun janjanta masa abinda ya faru da shi

A wani labari na daban, kungiyar matasan arewacin Najeriya (CNNY), ta bukaci tsohon gwamnan jihar Abia, gwamna Orji Uzor Kalu ya tsaya takarar shugabancin kasa a 2023.

Batun Wanda zai maye gurbin shugaban kasa Muhammad Buhari yana ta matsowa saboda saura shekaru 3 wa'adin mulkinsa ya cika.

Hakan zai bai wa 'yan kudancin Najeriya damar fitar da gwaninsu. Jiga-jigan jam'iyyar APC irin su Asiwaju Bola Tinubu ne ake sa ran zasu amshi kujerar mulki da zarar wa'adin shugaba Buhari ya kare a 2023.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel