2023: Mun amince da shugabancinsa - Matasan arewa sun bayyana zabinsu

2023: Mun amince da shugabancinsa - Matasan arewa sun bayyana zabinsu

- An roki Sanata Orji Kalu akan ya tsaya takarar shugaban kasa a 2023 idan wa'adin mulkin Buhari ya cika

- Wasu matasan arewa da ke karkashin wata kungiya ta CNNY sunyi kira gareshi a karon farko yayin da 2023 ke matsowa

- A yadda matasan suka ce, sun amince dari bisa dari da halayensa da kuma tsarin mulkin tsohon gwamnan jihar Abia

Kungiyar matasan arewacin Najeriya (CNNY), ta bukaci tsohon gwamnan jihar Abia, gwamna Orji Uzor Kalu ya tsaya takarar shugabancin kasa a 2023.

Batun Wanda zai maye gurbin shugaban kasa Muhammad Buhari yana ta matsowa saboda saura shekaru 3 wa'adin mulkinsa ya cika.

Hakan zai bai wa 'yan kudancin Najeriya damar fitar da gwaninsu.

Jiga-jigan jam'iyyar APC irin su Asiwaju Bola Tinubu ne ake sa ran zasu amshi kujerar mulki da zarar wa'adin shugaba Buhari ya kare a 2023.

CNNY ta ce zasu rike wuta yadda Kalu, wanda yanzu haka sanata ne daga jihar Abia zai maye gurbin shugaban kasa a 2023.

CNNY sun sanar da hakan a wata takardarsu ta ranar 1 ga watan Oktoba, wadda shugaban su Zarewa Salisu Sageer da sakataren su na kasa, Abu Bature Dandume suka sa hannu.

Kamar yadda takardar tazo, "sakamakon zurfin tunani, yasa muke rokon mai girma tsohon gwamnan jihar Abia kuma bulalar majalisa, Sanata Orji Uzor Kalu ya zo yayi takarar shugabancin kasa a shekarar 2023.

"Mun amince dashi, sakamakon hangen nesansa, salon mulkinsa, jajircewarsa, mun yarda zai kawo wa Najeriya cigaba mai tarin yawa."

KU KARANTA: Tsintar gawar mafarauci a daji ya tada hankulan mazauna Abia

2023: Mun amince da shugabancinsa - Matasan arewa sun bayyana zabinsu
2023: Mun amince da shugabancinsa - Matasan arewa sun bayyana zabinsu. Hoto daga Vanguard
Asali: UGC

KU KARANTA: Gwamnoni sun kai wa Zulum ziyara, sun janjanta masa abinda ya faru da shi

A wani labari na daban, Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan ya ce masu zargin gwamnatin Buhari da rashawa 'yan adawa ne.

Yayi maganar ne a taro na biyu da aka yi akan yaki da rashawa wanda ICPC ta shirya, Lawan ya ce gwamnatin Buhari ta jajirce wurin yaki da rashawa.

Shugaban majalisar tarayya ya ce a tuna lokacin da gwamnatin baya ta kira rashawa da "sata kawai".

Yace, "Ban san su ba, kuma ban san me suka dogara dashi ba. Kuma ba zanyi amfani da jita-jita ba, zanyi amfani da gaskiyar lamari ne. Ina so a nuna min ta inda rashawar wannan gwamnatin yafi na waccan."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel