Rufe sashin tsokaci a Twitter: 'Yan Najeriya sun caccaki Shugaba Buhari

Rufe sashin tsokaci a Twitter: 'Yan Najeriya sun caccaki Shugaba Buhari

- Ma'abota amfani da kafar sada zumuntar zamani ta Twitter sun caccaki shugaba Buhari tare fadarsa

- Fadar shugaban kasan ta wallafa yadda ta kaddamar da layin dogo wanda ya fara daga Itakpe har zuwa Warri

- Rufe sashin tsokacin ya janyo wa fadar shugaban kasa cece-kuce domin wasu sun zargesu da hana jama'a fadin ra'ayinsu

'Yan Najeriya sun caccaki shugaban kasa Muhammadu Buhari da fadarsa sakamakon rufe sashin tsokaci na shafinsu a Twitter da suka yi.

Shugaban kasar ya bayyana cewa ya kaddamar da titin jirgin kasa daga Itakpe zuwa Warri.

Amma kuma sai aka kulle sashin tsokacin a wallafar, lamarin da yasa 'yan Najeriya suka kasa fadin albarkacin bakinsu a kan al'amarin.

Yayin da wasu suka kushe wannan hukuncin na rufe sashin tsokacin, sauran sun ce ta yuwu shugaban kasan ya gaji da shakiyancin 'yan Najeriya ne.

KU KARANTA: 'Yan sanda sun damke 'yan fashi 7 da suka addabi jihar Adamawa (Hotuna)

Rufe sashin tsokaci a Twitter: 'Yan Najeriya sun caccaki Shugaba Buhari
Rufe sashin tsokaci a Twitter: 'Yan Najeriya sun caccaki Shugaba Buhari
Asali: Twitter

KU KARANTA: Nigeria @ 60: Buhari zai yi jawabi ga 'yan Najeriya daga Eagle Square

A wani labari na daban, a ranar Alhamis, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tabbatar da cewa kasar nan tana cikin mawuyacin hali a fannin tattalin arziki.

Ya ce hakan kuwa daidai yake da kowacce kasa domin kuwa dukkan duniya ne ake cikin wannan halin.

Buhari ya sanar da hakan ne a jawabinsa ga 'yan Najeriya a ranar da kasar ta cika shekaru 60 da samun 'yancin kai.

Shugaban kasar ya kara da amincewa da cewa, kasar na fuskantar matsalolin tsaro daban-daban a sassan kasar.

Ya ce, "A yau na tabbatar da cewa Najeriya tana cikin mawuyacin hali na tattalin azriki kuma hakan ce ta kasance ga kowacce kasa a fadin duniya. Muna fuskantar kalubalen tsaro a sassa daban-daban na kasar nan."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel