Gwamnoni sun kai wa Zulum ziyara, sun janjanta masa abinda ya faru da shi

Gwamnoni sun kai wa Zulum ziyara, sun janjanta masa abinda ya faru da shi

- Gwamna Fayemi na jihar Ekiti, da wasu gwamnoni 3 sunje Borno don jajantawa gwamnan Borno akan harin da 'yan bindiga suka kai masa

- Gwamna Fayemi ya ja kunnen Gwamna Zulum akan wajibcin kara kula mai tsanani saboda ba wannan ne karo na farko da aka kai masa hari ba

- Yace dole ne gwamnoni su kara dagewa wurin kawo karshen rashin tsaro a jihar Borno kafin 'yan bindiga su mamaye kasar baki daya

Gwamnan jihar Ekiti kuma shugaban kungiyar gwamnoni da gwamnoni 'yan uwansa sun jawa gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum kunne akan ya dinga tsananta tsaro musamman idan zai je wurare masu hadarin gaske, amma sai yace "ya batun mutane na na jihar Borno? Me zai faru dasu?" A wannan halin tashin hankalin dake Borno.

Fayemi yayi wannan maganar ne ranar Laraba yayin da ya jagoranci tafiya tare da gwamnan Sokoto, wanda shine mataimakin shugaban NGF, Atiku Bagudu na jihar Kebbi, wanda shine shugaban gwamnonin APC da kuma Simon Lalong na jihar Plateau, wanda yake shugabantar NGF, zuwa jihar Borno don jajantawa Zulum akan harin da 'yan ta'adda suka kai wa tawagarsa.

KU KARANTA: Fada a kan saurayi: Budurwa ta yi hayar 'yan daba, sun kashe budurwar saurayinta

Gwamnoni sun kai wa Zulum ziyara, sun janjanta masa abinda ya faru da shi
Gwamnoni sun kai wa Zulum ziyara, sun janjanta masa abinda ya faru da shi. Hoto daga @Dailytrust
Source: Twitter

"Wannan bashi bane karo na farko da ake kai maka hari, amma saidai kace ai Allah zai kare ka, ko da mun ce Prof ka kula da kanka, sai dai kace, Mutane na fa? Wajibi ne a matsayina na gwamna in kula da lafiyarsu kuma in tsare su," maganar Fayemi.

Gwamnan jihar Ekiti ya ce, "Ba'a dade ba ni da Zulum muka samu shugaban kasa, ka sanar dashi matsalolin tsaro da sojoji ke fuskanta da kuma faman da mutanen ka keyi da rashin tsaro idan zasu koma gidajensu da gonakin su."

Ya ce, "wajibi ne kowanne gwamna ya jajirce wurin ganin karshen rashin tsaro a jihar Borno"

Ya ce, "idan har bamu dage mun kawo karshen rashin tsaro a jihar Borno ba, abin zai cigaba har sai ya zagaye ko ina a fadin kasar nan."

KU KARANTA: Nigeria @ 60: FG ta bada umarnin toshe dukkan hanyoyin da za su kai Eagle Square

A wani labari na daban, Majalisar zartarwa ta tarayya (FEC) wacce shugaban kasa Muhammadu Buhari yake jagoranta a taronta na yau Laraba, ta amince da fitar da tiriliyan N13.08 a matsayin kasafin shekarar 2021.

Ministan kudi, kasafi da tsarin kasa, Hajiya Zainab Ahmed ce ta sanar da hakan a wani taro na manema labarai akan abinda majalisar zartarwar ta zartar a taron da aka yi a wani dakin taro dake fadar shugaban kasa, Abuja.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel