Idan kuka kara hakuri, Boko Haram za ta zama tarihi a gwamnatin Buhari - Buni

Idan kuka kara hakuri, Boko Haram za ta zama tarihi a gwamnatin Buhari - Buni

- Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni ya ba al'ummar Maiduguri tabbacin cewa Boko Haram ta kusa zama tarihi a mulkin Buhari

- Ta'addanci a shiyyar Arewa maso Gabas ya yi sanadiyar asarar rayukan sama da mutane 32,000 da asarar dukiyar N3.42trn a Borno, Adamawa da Yobe

- Mai Mala Buni ya ce abunda mayakan Boko Haram ba za su iya yi ba, shi ne, kawar da kokarin gwamnati na kawo karshen su

Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni ya ba da tabbacin cewa Boko Haram ta kusa zama tarihi a mulkin Buhari, kasancewar yan ta'adda ba za su iya fin karfin shugabanni da mabiyansu ba.

Buni ya bayyana hakan ne a ranar Talata a Maiduguri yayin jajantawa Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno, kan harin da Boko Haram ta kai wa tawagarsa a hanyar zuwa Baga.

KARANTA WANNAN: Ana shirin murnar Nigeria @60, gwamnatin Ogun ta sanya dokar ta baci

Ta'addanci a shiyyar Arewa maso Gabas ya yi sanadiyar asarar rayukan sama da mutane 32,000 da asarar dukiyar N3.42trn a Borno, Adamawa da Yobe tun daga shekarar 2009.

Idan kuka kara hakuri, Boko Haram za ta zama tarihi a gwamnatin Buhari - Buni
Idan kuka kara hakuri, Boko Haram za ta zama tarihi a gwamnatin Buhari - Buni - @GuardianNigeria
Source: Twitter

"Abu daya da yan ta'adda ba za su iya yi ba shine kawar da yakinin ku al'umar Borno, da ma sauran jihohi. Kuma ba za su iya kawar da kokarin gwamnati na kawo karshen su ba."

Haka zalika, Gwamna Zulum ya gana iyalan 'yan sanda da 'yan sa kai JTF wadanda aka rutsa da su a harin da aka kaiwa tawagarsa ranar Juma'a, a hanyarsa ta zuwa Baga.

Ya ziyarci shelkwatar rundunar 'yan sandan jihar da ke a Maiduguri a ranar Litinin inda ya jajantawa iyalan wadanda harin ya salwantar da rayukansu da jikkata su.

KARANTA WANNAN: UAE ta janye dokar haramta wa yan Nigeria shiga kasashen Larabawa

A yayin ziyarar, kwamishinan yan sanda, Bello Makwashi, ya zayyana sunayen jami'an rundunar da suka mutu sakamakon wannan hari.

Zawaran sun roki gwamnan da ya taimaka masu a wannan lokacin na jarabta. A nashi bangaren, gwamnan ya sha alwashin taimaka wa iyalan ta kowacce fuska.

A wani labarin, Hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawa ta gurfanar da Baturen Ilimi na karamar hukumar Sabon Birni, jihar Sokoto, Ishaka Abdullahi, bisa zarginsa da sace kudaden shirin ciyar da dalibai.

An gurfanar da Abdullahi ne a babbar kotun jihar Sokoto, akan zarginsa da aikata laifuka shida da suka hada da karbar kudi ta hanyar yin karya, da suka kai N429,000.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Online view pixel