Da duminsa: Ana shirin murnar Nigeria @60, gwamnatin Ogun ta sanya dokar ta baci

Da duminsa: Ana shirin murnar Nigeria @60, gwamnatin Ogun ta sanya dokar ta baci

- Gwamnatin jihar Ogun ta sanya dokar hana zirga zirga a fadin jihar daga karfe 10 na dare zuwa 6 na safiyar ranakun Laraba da Alhamis

- Haka zalika gwamnatin jihar, ta haramta zirga zirga a ranakun Alhamis da Juma'a, daga karfe 10 na dare zuwa karfe 6 na safiya

- Gwamnatin jihar ta ce hakan ya zama wajibi ne la'akari da yadda annobar COVID-19 ta ke ci gaba da yin barna, tana mai nuna bukatar daukar matakan kariya

Gwamnatin jihar Ogun a ranar Laraba ta sanar da kakaba dokar ta baci a fadin jihar daga karfe 10 na dare zuwa karfe 6 na safe, a ranakun Laraba da Alhamis.

Haka zalika gwamnatin jihar, ta haramta zirga zirga a ranakun Alhamis da Juma'a, daga karfe 10 na dare zuwa karfe 6 na safiya.

KARANTA WANNAN: UAE ta janye dokar haramta wa yan Nigeria shiga kasashen Larabawa

Duk da cewa gwamnatin jihar ba ta bayar da dalili na kakaba dokar ta bacin ba, sai dai ba zai rasa nasaba da matsalar tsaro ba, da kuma rahotannin cewa wasu kungiyoyi za su gudanar da zanga zanga a ranar 1 ga watan Oktoba.

Da duminsa: Ana shirin murnar Nigeria @60, gwamnatin Ogun ta sanya dokar ta baci
Da duminsa: Ana shirin murnar Nigeria @60, gwamnatin Ogun ta sanya dokar ta baci - @nigeriantribune
Source: Twitter

A cewar sanarwar da aka wallafa a shafin gwamnatin jihar @OGSGOfficial: "An sanya dokar hana zirga zirga a jihar Ogun, daga karfe 10 na dare zuwa 6 na safiya, daga gobe Alhamis.

A safiyar yau ne dai gwamnatin jihar ta gudanar da wani dan karamin taron murnar cika shekaru 60 da samun 'yancin Nigeria.

KARANTA WANNAN: An gurfanar da Baturen Ilimi da ya sace N429,000 daga kudin ciyar da dalibai

Gwamnatin jihar ta ce hakan ya zama wajibi ne la'akari da yadda annobar COVID-19 ta ke ci gaba da yin barna, tana mai nuna bukatar daukar matakan kariya, tsaro da kuma lafiyar al'umma.

A wani labarin, Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya maye gurbin wasu jakadun Nigeria guda biyu da ya kai sunansu gaban majalisar dattijai amma ba a tantance su, ya kawo sabbin mutane biyu.

Ya maye gurbin Peter Gana (Niger) da Muhammed Manta (Niger), sai kuma Yusuf Mohammed (Yobe) da Yusufu Yunusa (Yobe).

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel