Da duminsa: UAE ta janye dokar haramta wa yan Nigeria shiga kasashen Larabawa

Da duminsa: UAE ta janye dokar haramta wa yan Nigeria shiga kasashen Larabawa

- Daular kasashen daular Larabawa, ta amince da janye dokar haramtawa 'yan Nigeria 'Visa', a cewar Ministan sufurin jiragen sama, Hadi Sirika

- Daular UAE ta janye wannan dokar hana 'Visa' ne bayan da Nigeria ta ce, ba za ta bar jiragen daular su yi aiki a Nigeria ba

- Wannan ya biyo bayan dakatar da sufurin jiragen sama na kasashen Turai, idan aka cire kamfanin jiragen Bristish Airways a Nigeria

Daular kasashen daular Larabawa, ta amince da janye dokar haramtawa 'yan Nigeria Visa. Ministan sufurin jiragen sama, Hadi Sirika, ya sanar da hakan a ranar Laraba.

Sirika ya bayyana cewa Nigeria ta kuma amince kamfanin jiragen sama na daular Larabawa 'Emirates Airlines' ya dawo da aiki a Nigeria.

A cewar sa, daular kasashen Larabawan ta janye wannan dokar hana 'Visa' ne bayan da Nigeria ta ce, ba za ta bar jiragen daular su yi aiki a Nigeria ba, ma damar ba ta janye haramcin ba.

KARANTA WANNAN: An gurfanar da Baturen Ilimi da ya sace N429,000 daga kudin ciyar da dalibai

Da duminsa: UAE ta janye dokar haramta wa yan Nigeria shiga kasashen Larabawa
Da duminsa: UAE ta janye dokar haramta wa yan Nigeria shiga kasashen Larabawa - @MobilePunch
Asali: Twitter

Ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa, "UAE ta aiko da sanarwar cewa za su dawo ba wa yan Nigeria 'Visa', haka zalika za a kyale jiragen su suyi aiki a Nigeria.

"Za a dawo bayar da 'Visa' din ne akan yarjejeniya. Muna fatan 'yan Nigeria su yi hakuri da matsalar da aka fuskanta. Muna godiya."

Gwamnatin tarayya a baya ta haramtawa kamfanin jiragen Emirates Airlines yin aiki a Abuja da Lagos, bisa zargin daular Larabawan da datakar da ba da 'Visa' ga yan Nigeria.

KARANTA WANNAN: Buhari ya yi manyan nade nade, ya aika wa majalisa da sunaye

Wannan ya biyo bayan dakatar da sufurin jiragen sama na kasashen Turai, idan aka cire kamfanin jiragen Bristish Airways a Nigeria.

Kafin dawo da ci gaba da sufurin jiragen sama a Nigeria, gwamnatin tarayya ta sanar da cewa ba ta lamuncewa Air France, KLM, Etihad, RwandAir, Air Namibia, Royal Air Maroc, Lufthansa, TAAG Angola Airlines yin aiki a kasar ba.

Haka zalika an haramtawa Cabo Verde da South African Airlines yin jigilar mutane, domin shigowa ko fita daga Nigeria.

Tun farko, kungiyar UAE ta ce an samu tsaikon zirga zirga tsakanin Nigeria da UAE sakamakon rufe iyakokin saman Nigeria.

UAE ta karyata zargin cewa ta haramtawa 'yan Nigeria Visa, tana mai cewa, a ranar 17 ga watan Maris 2020 ne ta haramta ba da Visa ga kowacce kasa, domin dakile yaduwar COVID-19.

A wani labarin, Hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawa ta gurfanar da Baturen Ilimi na karamar hukumar Sabon Birni, jihar Sokoto, Ishaka Abdullahi, bisa zarginsa da sace kudaden shirin ciyar da dalibai.

An gurfanar da Abdullahi ne a babbar kotun jihar Sokoto, akan zarginsa da aikata laifuka shida da suka hada da karbar kudi ta hanyar yin karya, da suka kai N429,000.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel