Nigeria @ 60: Buhari zai yi jawabi ga 'yan Najeriya daga Eagle Square

Nigeria @ 60: Buhari zai yi jawabi ga 'yan Najeriya daga Eagle Square

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa, daga Eagle Square zai yi wa 'yan Najeriya jawabi

- Hadiminsa, Femi Adesina ne ya sanar da hakan ana jajberin ranar cikar kasar shekaru 60 da samun 'yancin kai

- Ya bayyana cewa, za a saurari jawabin kai tsaye a gidan talabijin na NTA da rediyo na FRCN a ranar Alhamis

Daga cikin shagulgulan cikar Najeriya shekaru 60 da samun 'yancin kai, Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai yi jawabi ga 'yan Najeriya a Abuja, ranar Alhamis 1 ga watan Oktoba, 2020.

An sanar da hakan a wata takarda da mai bada shawara na musamman ga Shugaban kasa akan yada labarai, Femi Adesina ya sa hannu. Shugaban kasa zai yi jawabin ne bayan anyi faretin zagayowar shekarar.

"Za'a fara nuna jawabin shugaban kasa a tashoshin talabijin da gidajen radiyo bayan an gama fareti karfe 10am daidai, musamman NTA da FRCN," kamar yadda takardar tazo.

KU KARANTA: Rikicin APC a Ekiti: El-Rufai, Wase da Okorocha sun jagoranci kwamitin sulhu

Nigeria @ 60: Buhari zai yi jawabi ga 'yan Najeriya daga Eagle Square
Nigeria @ 60: Buhari zai yi jawabi ga 'yan Najeriya daga Eagle Square. Hoto daga @Lindaikeji
Asali: Twitter

KU KARANTA: Zukekiyar budurwa ta wallafa hotonta tana neman saurayi, ta ce kada talakan da ya kawo kansa

A wani labari na daban, Gwamnatin tarrayya ta bada umurnin dakatar da shige da fice a duk wasu hanyoyin da zasu kai Eagle square tun daga tsakar daren Laraba, 30 ga watan Satumba, don shiryawa bikin murnar cikar Najeriya shekaru 60 da samun 'yancin kai da za a yi a ranar Alhamis, 1 ga watan Oktoba.

Ministan yada labarai da al'adu, Lai Muhammad ne ya sanar da hakan domin tabbatar da tsaron ciki da wajen Eagle square, inda aka tsara yin shagalin bikin a cikin babban birnin tarayya, Abuja.

Sannan kuma, za'a dakatar da shiga titin Shehu Shagari, titin Ahmadu Bello, titunan shige da ficen tashoshin jiragen sama, duk wasu titunan dake haduwa da shiga babbar sakateriyar tarayya daidai karfe 2.00pm a ranar Laraba, 30 ga watan Satumba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel