Fada a kan saurayi: Budurwa ta yi hayar 'yan daba, sun kashe budurwar saurayinta

Fada a kan saurayi: Budurwa ta yi hayar 'yan daba, sun kashe budurwar saurayinta

- Wata mata Rebecca Masawi tayi hayar yan daba 3 don ladabtar da 'yan matan dake bibiyar saurayinta

- 'Yan daban sun yi shiga irinta 'yan sanda, inda suka je har gida suka yi musu sata kuma suka kashe su

- Yanzu haka Rebecca da 'yan daban ta suna fuskantar tuhumar wadanda suka kashe rai a kotu

Wata mata yar kasar Zimbabwe na fuskantar tuhumar kashe rai sakamakon hayar 'yan daba su zane yan matan saurayinta.

Rebecca Masawi da 'yan daban da tayi haya guda 3, Zvikomborero Zvikoni, Liberty Guruve da kuma Tendai Dhai suna gaban kotu, akan laifin kinsan kai, garkuwa da mutane da kuma fashi, bayan sun cutar da wata mata har ta mutu.

Kamar yadda takardun kotu suka bayyana, ran Masawi yayi mummunan baci akan wasu 'yan mata dake bibiyar saurayinta, sai wata dabara tazo mata.

Ba'a fadi sunayen 'yan matan da aka kashe ba a takardun kotu.

An samu rahoton yadda Masawi da 'yan daban ta suka je gidan 'yan matan tsakar daren 31 ga watan Yuli, 2020 da wasu motoci marasa lamba a jikinsu.

'Yan daban sun nuna kamar su yan sanda ne, sai suka bankada kofar gidan, suka koro 'yan matan da tsallen kwado har suka shiga motocin.

'Yan daban sun yashe gidan tsaf, har suna sace musu abubuwan su masu muhimmanci.

Bayan shigar 'yan matan mota, sai 'yan sandan bogin suka wuce dasu wurin tafkin Chivero inda sukayi ta gana musu azaba.

Sun yi musu azaba iri-iri har da karya kafafun su.

Masu wucewa ne suka samu damar ceto 'yan matan suka kuma kira 'yan sanda take a nan.

'Yan sanda sun dauki 'yan matan cikin mummunan yanayi, suka kaisu asibitin Parirenyatwa kafin a wuce dasu babban asibitin Chitungwiza, inda aka yi musu aiki kuma aka sallamesu a ranar 3 ga watan Ogusta,2020.

Duk da aikin, sai da daya ta rasa ranta sakamakon munanan raunukan da suka ji mata.

Yan sanda sun kwashe wata daya suna bincike akan al'amarin, har suka gano Zvikoni na amfani da wayar matar da ta mutu.

An kamashi ranar 26 ga watan Satumba bayan anyi masa tambayoyi. Ya sanar da cewa, ba shi kadai yayi aika-aikar ba, har da Guruve da Dhai.

Ya kuma yi karin bayani akan yadda al'amarin ya faru, har ya sanar da cewa hayarsu Rebecca Masawi tayi.

Rebecca Masawi ta bayyana gaban kotun majistare a ranar Litinin, 28 ga watan Satumba don fuskantar laifukanta.

KU KARANTA: Jirgin farko a duniya da ke amfani da iskar Hydrogen ya fara aiki a Ingila (Bidiyo)

Fada a kan saurayi: Budurwa ta yi hayar 'yan daba, sun kashe budurwar saurayinta
Fada a kan saurayi: Budurwa ta yi hayar 'yan daba, sun kashe budurwar saurayinta. Hoto daga @Vanguard
Source: Twitter

KU KARANTA: Masu zargin gwamnatin Buhari da cin rashawa manyan 'yan adawa ne - Lawan

A wani labari na daban, ba'a ritsa mako biyu ba da wata budurwa ta tsugunna har kasa don amsar zoben sa ranar auren ta, wata budurwa ma ta bi sahun ta.

Wata budurwa, Angel Nwedo, ta wallafa hoton sa ranar aurenta cikin farinciki. Maimakon saurayin ya tsugunna ya mika mata zobe kamar yadda aka saba, kawai sai ga budurwar a kasa tana amsar zoben cike da annashuwa.

Wannan al'amarin yazo ne babu dadewa bayan hotunan wata budurwa mai suna Adaeza Gift Okolie, sun karade kafar sada zumunta.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel