Da duminsa: Buhari ya yi manyan nade nade, ya aika wa majalisa da sunaye

Da duminsa: Buhari ya yi manyan nade nade, ya aika wa majalisa da sunaye

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari, a ranar Talata ya yi manyan nade nade da suka shafi bangarori uku na gwamnatin Nigeria

- Bangaren farko shine musanya sunayen jakadun Nigeria guda biyu daga jihar Niger da Yobe da majalisar ta ki tantancewa da wasu sabbi

- Sai kuma nadin sabbin shuwagabannon hukumar kiyaye kayayyakin amfanin al'umma na kasa da hukumar fansho ta kasa

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya maye gurbin wasu jakadun Nigeria guda biyu da ya kai sunansu gaban majalisar dattijai amma ba a tantance su, ya kawo sabbin mutane biyu.

Ya maye gurbin Peter Gana (Niger) da Muhammed Manta (Niger), sai kuma Yusuf Mohammed (Yobe) da Yusufu Yunusa (Yobe).

KARANTA WANNAN: Maimakon korafi: Ku taya ni yakar cin hanci da rashawa - Buhari ga 'yan Nigeria

Da duminsa: Buhari ya yi manyan nade nade, ya aika wa majalisa da sunaye
Da duminsa: Buhari ya yi manyan nade nade, ya aika wa majalisa da sunaye
Source: Twitter

Wannan sabon nadin na kunshe a cikin wata wasika da shugaban kasar ya aikewa shugaban majalisar dattijai, kuma Ahmad Lawan, ya karanta a zaman majalisar na ranar Talata.

"Bisa amfani da sashe na 171(1)(2)(c) da kuma karamin sashe na (4) na dokar Nigeria ta 1999 kamar yadda aka sabunta, ina gabatar maku da wadannan sunayen don tantancewa.

"Ina rokon majalisar ta amince da nadin Ambasada Muhammad Haruna Manta da Yusufu Yunusa da suka fito daga jihohin Niger da Yobe, a matsayin nadaddun jakadun Nigeria.

"Tare da wannan wasikar, akwai takardun karatu da bayanin ayyukansu (CV), domin nazari da tantancewar ku.

"Ina fatan majalisar dattijan za ta tuna sunayen Air Commodore Peter Ndabake Gana (RM) da Alh. Yusuf Mohammad, da na gabatar, amma ba su samu tsallake tantancewar majalisar ba.

"Rashin amincewar ku akan sunayen ne, ya sa na kawo madadinsu a yau, Amb. Muhammad Haruna Manta zai maye gurbin Air Commodore Peter Ndabake Gana, daga jihar Niger.

"Haka zalika, Yasufu Yunusa zai maye gurbin Alh. Yusuf Mohammad, da suka fito daga jihar Yobe, ina fatan majalisar za ta amince da wannan nadi," a cewar wasikar.

KARANTA WANNAN: Matasa a yi hattara: Kotu ta garkame mashayin wiwi bayan kamashi da ita a Kano

Wasu nade naden:

A wani ci gaban, shugaban kasa Buhari ya aikewa majalisar dattijai da sunayen mutane 8 don nada su mukaman shugaba, mataimakin shugaba, babban kwamishina, karamin kwamishina, na hukumar kiyaye kayayyakin amfanin al'umma na kasa (FCCPC).

Su ne; Emeka Nwankpa (Shugaban Kudu maso Gabas), Babatunde lrukera (Mataimakin shugaban Arewa ta tsakiya), Yinka Osoba Apata (Shugaban Kudu maso Yamma) da kuma Adamu Ahmed Abdullahi (Shugaban Arewa maso Gabas)

Sauran sun hada da Wakili Abdullahi Ahmed (Karamin kwamishinan Arewa maso Yamma), Ayang Francis Eyam (Karamin kwamishinan Kudu maso Kudu).

Ben Nwoye (Karamin kwamishinan Kudu maso Gabas) da kuma Theophilus Oyebiyi (Karamin kwamishinan Arewa ta tsakiya)

Shugaban kasa Buhari ya kuma aikewa majalisar dattijan bukatar amincewa da nadin mutane shida a mukamin shugaba, darakta janar da kuma kwamishinonin hukumar fansho ta kasa.

A wani labarin, Gwamnatin tarayya ta kaddamar da sabon shafin yanar gizo tare da manhajar wayar hannu, a shirin mayar da ayyukan gwamnatin Nigeria a tsarin yanar gizo.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya kaddamar da wannan shiri na Nigeria a yanar gizo (DNP) a ranar 19 ga watan Maris, 2020.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel