Babu hannun ma'aikatar walwala wurin wawure N2.67b - ICPC ta yi karin bayani

Babu hannun ma'aikatar walwala wurin wawure N2.67b - ICPC ta yi karin bayani

- Hukumar ICPC ta yi karin bayani akan maganar shugaban ICPC, Bolaji akan ciyar da dalibai a gida

- Bincike ya nuna cewa Naira Biliyan 2.67 da ya kamata a ciyar da dalibai ta bata ne cikin asusun bankunan wasu

- Ana cigaba da bincike akan asusun bankuna da ake zargi da kalmashe kudaden ciyar da dalibai lokacin kullen Covid-19

Hukumar ICPC ta yi karin bayani akan maganar da Bolaji Owasanoye, shugaban hukumar yayi, akan zargin waskar da biliyan N2.67 na kudin ciyar da 'yan makaranta.

Ranar Litinin aka yi taron kawar da rashawa, inda Owasanoye yace, ICPC ta bi naira biliyan 2.67 da yakamata ayi amfani dasu wurin ciyar da daliban makarantun gwamnati, inda aka gano kudaden a cikin asusun bankunan wasu.

Owasanoye yace, "Mun gano kudaden da yakamata ayi amfani dasu wurin ciyar da dalibai Naira biliyan 2.67 lokacin kulle, duk da yara na gidajensu, sai muka ga kudaden a asusun bankunan wasu. Yanzu haka mun dage da bincike akan wadannan kudaden."

Amma Azuka Ogugua, kakakin ICPC ya ce a wata takarda, sai da suka yi karin bayani akan maganar Owasanoye, har an fara fassara shi da amfani da kudaden wurin ciyar da yara duk da suna gida wadda ma'aikatar jin kai da walwalar 'yan kasa ta jagoranta.

Takardar tayi bayani akan kudaden da ya kamata ayi amfani da su wurin ciyar da daliban makarantun gwamnati na kwana dake fadin kasar nan.

Hukumar ta kara bayani akan "ciyar da dalibai" na nufin ciyar da daliban makarantun kwanan gwamnatin tarayya, ba wai wadanda suke gida lokacin da ake kullen annobar Coronavirus ba.

Ya ce, "Wannan ciyarwar ta ma'aikatar walwala da jin kai ba don ciyar da dalibai yayin da suke gida bane.

"Wannan takardar an rubuta ta ne saboda karin bayani akan maganar shugaban. Don haka ana jawo hankalin al'umma da kada su yarda da wannan batun na ciyar da daliban firamare."

KU KARANTA: Allah ya yi wa Sarkin Kuwait, Sheikh Sabah, rasuwa

Babu hannun ma'aikatar walwala wurin wawure N2.67b - ICPC ta yi karin bayani
Babu hannun ma'aikatar walwala wurin wawure N2.67b - ICPC ta yi karin bayani. Hoto daga @Thepunch
Source: UGC

KU KARANTA: Magidanci ya halaka kwarton matarsa bayan kama su da yayi suna lalata a kan gadonsu na aure

A wani labari na daban, Sadiya Umar Farouq ta ce ma'aikatar tallafi da jin kai bata da alaka da damfarar N2.67 biliyan na ciyar da 'yan makaranta, wacce hukumar yaki da rashawa mai zaman kanta (ICPC) ta bankado.

A ranar Litinin, ICPC ta sanar da cewa an bankado wasu N2.67 biliyan wacce gwamnatin tarayya ta biya domin ciyar da 'yan makaranta, a wasu asusun bankuna masu zaman kansu.

Amma a wata takarda da Nneka Ikem Anibeze, mai bada shawara na musamman a fannin yada labarai ga Umar Farouq, ta ce wannan ciyarwar da ake magana tana da banbanci da wacce ake yi a karkashin ma'aikatar walwala da jin kai.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel