Matasa a yi hattara: Kotu ta garkame mashayin wiwi bayan kamashi da ita a Kano

Matasa a yi hattara: Kotu ta garkame mashayin wiwi bayan kamashi da ita a Kano

- Wata kotun Majistire a Kano ta yanke wa wani matashi hukuncin zaman gidan wakafi, bayan samunsa da tabar wiwi da miyagun kwayoyi

- Mai Shari'a Malam Farouk Ibrahim ya yankewa Bashir da aka cafke a kasuwar Kantin Kwari wannan hukunci ba tare da zabin biyan tara ba

- Bashir Ibrahim ya amsa laifinsa na mallakar molin ganyen tabar wiwi guda 17 da kuma kwayoyin Diazepam guda 29

Wata kotun Majistire a Kano, a ranar Talata ta yankewa Bashir Ibrahim (25) hukuncin watanni bakwai a gidan gyara hali, bayan kama shi da tabar wiwi da sauran miyagun kwayoyi.

Ibrahim, wanda ke da zama a rukunin gidajen Fagge, Kano, ya amsa laifinsa na mallakar kwayoyin Diazepam guda 29, da kuma tabar Wiwi, lamarin da ya sa aka yanke masa hukuncin.

Mai Shari'a Malam Farouk Ibrahim ya yankewa Bashir wannan hukunci na zaman gidan gyara hali na tsawon watanni bakwai, ba tare da zabin biyan tara ba.

KARANTA WANNAN: Munafukai daga cikin mukarrabanka ne ke jawo maka zagi - Shawarar Okorocha ga Buhari

Matasa a yi hattara: Kotu ta garkame mashayin wiwi bayan kamashi da ita a Kano
Matasa a yi hattara: Kotu ta garkame mashayin wiwi bayan kamashi da ita a Kano - @nigeriantribune
Source: Twitter

Ya ce wanda aka yankewa hukuncin, na da ikon daukaka kara nan da kwanaki talatin.

Tun farko, jami'i mai shigar da kara, Mr Mubarak Mukhtar, ya shaidawa kotun cewa wanda ake zargin ya aikata laifin a ranar 23 ga watan Satumba, a kasuwar Kwari, jihar Kano.

KARANTA WANNAN: FG ta buɗe sabon shafin yanar gizo, ta ƙirƙiri manhajar wayar hannu - Pantami

Ya ce rundunar 'yan sanda da ke ofishin rundunar na Fagge, ta cafke wanda ake zargin a yayin da jami'anta ke rangadi a babban kantin Yan-Tebura, cikin kasuwar Kwari, jihar Kano.

"A lokacin sumamen, an cafke wanda ake zargin da miyagun kwayoyi da suka da tabar wiwi, kwayoyin Diazepam guda 29 da kuma wata tabar guda 17."

Jami'in ya ce wannan laifin ya ci karo da doka ta sashe na 403 da ke a cikin dokokin aikata laifuka na jihar Kano, a cewar kamfanin dillacin labarai na kasa, NAN.

A ranar Litinin, kwararru a Majalisar Dinkin Duniya sun bukaci Nigeria da ta saki mawakin da aka yankewa hukuncin kisa saboda zarginsa da batanci ga Annabi Muhammad (SAW).

A watan da ya gabata ne wata kotun shari'a a Kano, ta yankewa Yahaya Aminu Sharif hukuncin kisa, bayan da ya yi wakar batanci ga Musulunci da Annabi, kuma ya raba a WhatsApp.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Online view pixel