Allah ya yi wa Sarkin Kuwait, Sheikh Sabah, rasuwa

Allah ya yi wa Sarkin Kuwait, Sheikh Sabah, rasuwa

- Sarkin Kuwait mai shekaru 91 ya rasu ranar Talata 29 ga watan Satumba

- Rasuwar Sheikh Sabah Al-Ahmad ta girgiza mutane da dama

- Sheikh Ali Jarrah Al-Sabah, ministan yada labarai ne ya sanar da mutuwar

Sarkin Kuwait mai shekaru 91 da haihuwa, Sarki Sabah Al-Ahmad Al-Sabah ya rasu ranar Talata a wani asibiti a Amurika.

"Muna bakin cikin sanar da mutuwar Sheikh Sabah Al-Ahmad Al-jaber Al-Sabah, sarkin Kuwait," inji Sheikh Ali Jarrah Al-Sabah, ministan yada labaran kasar.

An haifi Sheikh Sabah a shekarar 1929, ya rike kujerar ministan harkokin kasashen waje na tsawon shekaru 40, tsakanin 1963 zuwa 2003 daganan ya zama shugaban kasa.

Ya zama sarkin Kuwait a watan Janairu, 2006 bayan rasuwar Sheikh Jabeer Al-Sabah.

A watan Augusta 2019 an sanar da rashin lafiyarsa duk da ba'a fadi cutar da ke damunsa ba, har ta kai ga an kwantar da shi a asibiti.

An fitar dashi Amurka don duba lafiyarsa a watan Yulin 2020.

KU KARANTA: Zan bai wa 'yan Najeriya kariya ba tare da duba banbancin jam'iyya ba - Buhari

Allah ya yi wa Sarkin Kuwait, Sheikh Sabah, rasuwa
Allah ya yi wa Sarkin Kuwait, Sheikh Sabah, rasuwa. Hoto daga @Aljazeera
Source: Twitter

KU KARANTA: Dakarun soji sun tsananta wa 'yan bindiga, sun ragargaza maboyarsu a Borno

A wani labari na daban, Labari da duminsa da ke zuwa wa Legit.ng shine rasuwar Sarkin Zazzau, Alhaji Shehu Idris. Majiyoyi da dama da suke da kusanci da fadar sarkin sun tabbatar da rasuwarsa a yau Lahadi.

Marigayi Sarkin Zazzau shine Sarki na 18 na Fulani a masarautar Zazzau. Ya rasu yana da shekaru 84 a duniya.

Majiyoyi da dama sun tabbatar wa Legit.ng cewa, basaraken ya rasu a asibitin 44 da ke Kaduna wurin karfe 11 na safiyar Lahadi.

"Tabbas Allah ya yi wa Sarki rasuwa. Ya kwanta rashin lafiya tun a ranar Juma'a kuma an kai shi asibiti inda ya rasu.

"Nan babu dadewa za a dawo da gawarsa Zaria domin fara shirin jana'izarsa," wata majiya mai kusanci da Iyan Zazzau ta tabbatar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel