Allah ke ciyarwa, zan cigaba da haihuwa - Mutumin da ke da 'ya'ya 19 (Bidiyo)

Allah ke ciyarwa, zan cigaba da haihuwa - Mutumin da ke da 'ya'ya 19 (Bidiyo)

- Kukat Kamartum dan kauyen Riong'o, tare da matansa 3 da yara 19 suna zama a wani kango, ya ce yara arziki ne, kuma yana fatan yaransa su kara yawa

- Mutumin yace Ubangiji ne mai badawa, kuma bai taba damun kansa akan matsalolin rayuwa ba, kamar abinci, magani da ilimi

- Matan Kamartum 3 sunce basu da labarin ana shan maganin tsarin iyali, ko kuma akwai hanyoyin tsara iyali na musamman ba

Wani mutumi mai shekaru 33, dan Baringo yana da yara 19, ya ce yara arziki ne nan gaba.

Kukat Kamartum dan kauyen Riong'o, dake Baringo yana da mata 3 dake zaune tare, a wani dan kango inda suke kiwon tumaki da awaki 100.

Kamartum yayi maganar nan ne ranar Lahadi, 27 ga watan Satumba, ranar tsara iyali ta duniya. Ya ce yana bukatar wasu yaran, saboda yana ganin zai iya azurcewa saboda yaran nan gaba.

Yace, "Misali kana da yara mata 10 kuma aurensu ya tashi, za'a iya bada shanu 10 zuwa 15 saboda kowacce yarinya, kuma ana bada rakumai 4 akan kowacce yarinya, idan ka kirga, rakumai 40 kenan, kaga kuwa wannan dukiya ce mai yawa."

Mutumin yace bai taba damuwa ba akan ciyar dasu, lafiyarsu da iliminsu, saboda Ubangiji ne yake yin komai.

Da aka yi hira da matansa guda 3, cewa suka yi basu san ana tsarin iyali ba, balle har su san ana amfani da wasu magunguna.

Su dai haihuwa kawai sukeyi, duk lokacin da ta kama. "Bamu taba jin labarin wani tsarin iyali ba," cewar uwargidan sa.

KU KARANTA: Katsina da Zamfara: 'Yan bindiga 32 sun shiga hannu, an kashe 1 - DHQ

Allah ke ciyarwa, zan cigaba da haihuwa - Mutumin da ke da 'ya'ya 19 (Bidiyo)
Allah ke ciyarwa, zan cigaba da haihuwa - Mutumin da ke da 'ya'ya 19 (Bidiyo). Hoto daga Daily Times
Source: UGC

KU KARANTA: Dakarun soji sun tsananta wa 'yan bindiga, sun ragargaza maboyarsu a Borno

A wani labari na daban, wani tsari na jera kasashen da suke da saukin samun ayyuka na shekarar 2020 ya fita, inda kasashe 5 na farko suka bayyana.

Cikin kasashe 5 na sama kuwa Ingila ce kasar farko a jerin, yayin da Jamus ta biyu, Canada kuwa ta samu fitowa a ta uku. Amurka tazo a ta hudu, Japan tazo a ta biyar.

A dayan bangaren kuwa, Najeriya tana can kasan jerin tare da Yemen, Syria da Libya. Wani shafi na Twitter mai suna Nairalytics, ya wallafa jerin kasashen bayan tsananin bincike da nazari akan kasashen guda 127.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel