Munafukai daga cikin mukarrabanka ne ke jawo maka zagi - Shawarar Okorocha ga Buhari

Munafukai daga cikin mukarrabanka ne ke jawo maka zagi - Shawarar Okorocha ga Buhari

- Rochas Okorocha ya yi kira ga shugaban kasa Buhari da ya dauki kwakkwaran mataki kan hadimansa wadanda ba sa aikin azo a gani

- Tsohon gwamnan Imo wanda ya yi ikirarin cewa akwai wasu da ke rike da mukaman gwamnati da ke jawowa shugaban kasar zagi da bakin jini

- Okorocha ya sanar da hakana ranar Litinin, yayin wani taro na kwamitin shuwagabannin jam'iyyar APC da kwamitin gudanarwar jam'iyyar na kasa

Tsohon gwamnan jihar Imo, kuma Sanata mai wakiltar Imo ta Yamma, Rochas Okorocha ya yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya dauki kwakkwaran mataki kan hadimansa.

Rochas Okorocha, ya shawarci shugaban kasar, kan mukarrabansa da ba sa tsinana komai a bangarorin da aka nada su.

KARANTA WANNAN: Majalisar Dinkin Duniya na son a yafe wa wanda da ya yi batanci ga Annabi a Kano

Munafukai daga cikin mukarrabanka ne ke jawo maka zagi - Shawarar Okorocha ga Buhari
Munafukai daga cikin mukarrabanka ne ke jawo maka zagi - Shawarar Okorocha ga Buhari - @Nigeriantribune
Source: Twitter

Ya bayar da wannan sanarwar ne a ranar Litinin, yayin wani taro na kwamitin shuwagabannin jam'iyyar APC da kwamitin gudanarwar jam'iyyar na kasa.

Tsohon gwamnan Imo wanda ya yi ikirarin cewa akwai wasu da ke rike da mukaman gwamnati da ke jawowa shugaban kasar zagi, saboda rashin kyautawar da suke yiwa mutane.

KARANTA WANNAN: APC ta yi babban rashi a jihar Delta, tsohon gwamna ya koma PDP

A cewar sa, "Ya zama wajibi in sanar da ku cewa a kasashen da suka ci gaba, ana daukar aiki da kora ne don ladabtarwa. Ma damar ba ka yin aikin azo a gani, to ba ka da amfani a gwamnati.

Ire iren wadanda masu rike da mukaman gwamnatin da ba sa tsinana komai ya kamata a sallame su, idan ba za ka iya ba, akwai wadanda za su iya.

"A yanzu kowanne mai rike da mukami baya tunanin al'umma, tunanin sa zabe na gaba, da tunanin mukamin da zai sake samu, ba wai taimakon jama'ar Nigeria ba."

A wani labarin, gwamnan jihar Kaduna, Nasiru Elrufai ya musanta labarin da ake yadawa a kafafen watsa labarai na cewar ya karbi sunaye daga masu zaben sarkin Zazzau.

A cewar gwamnan, wannan labarin kanzon kurege ne kawai, kasancewar har yanzu, babu wani suna da ya zo gabansa, da sunan tantancewa don nada sabon sarki.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel