Yadda bakanike ya tsere da motar kwastoma daga kai masa gyara

Yadda bakanike ya tsere da motar kwastoma daga kai masa gyara

- Wani mawaki ya wallafa hotunan motarsa da hoton wani bakanike da ke jihar Imo

- Kamar yadda ya sanar, bakaniken na kan hanya ne kuma ya tsere musu da mota bayan bashi gyara da suka yi

- Ya ce daga tattaba motar, sai yace bari ya gwada ko tayi, daga nan yayi batan dabo da ita

Wani bakaniken kan hanya dake unguwar Nkwola Eziama a jihar Imo ya gudu da motar wadanda suka bashi gyara.

Kamar yadda wani mawaki ya wallafa ranar Asabar, 26 ga watan Satumba, wata Chinyere Ezeji ta ce motarsu ta tsaya a wuraren layin Amala/Eziama ranar Juma'a.

Sai suka dakata wurin bakaniken kan hanyar Nkwola-Eziama, mai suna Chukwudi don ya gyara musu motar.

Bayan ya tattaba motar, sai yace bari ya zagaya da ita don ya tabbatar ko gyaran yayi, daga nan ba'a sake ganinshi ba.

"Muna hanyar zuwa kauyenmu ta'aziyya da motar Rev. Cyril Nwaelele, sai motar ta samu matsala a hanyar Amala/Eziama.

"Wasu mutanen kirki suka taimakemu wurin tura motar zuwa Nkwola-Eziama, inda muka samu bakanike wanda yayi kokarin gyara motar daga nan ya wuce da ita.

"Mun samu labarin sunan mutumin Chukwudi kuma dan Omoku ne. Don Allah, idan an samu wanda ya sanshi, ya taimakemu mu amso motar", yace.

KU KARANTA: Gurfanar Obasanjo a gaban tsoho mai shekaru 94 ya janyo cece-kuce

Yadda bakanaike ya tsere da motar kwastoma daga kai masa gyara
Yadda bakanaike ya tsere da motar kwastoma daga kai masa gyara. Hoto daga @Lindaikeji
Asali: Twitter

KU KARANTA: Yadda 'yan kungiyar asiri suka makantar da ni saboda na ki shiga kungiyarsu - Matashi

A wani labari na daban, kakakin rundunar yan sandan jihar Anambra, Muhammad Haruna, yace suna irin wannan kamen saboda damkar masu laifi musamman na kungiyar asiri a wuraren da ake zargin maboyarsu ne.

Yace an kama mutane 15 da ake zargi a tsakanin Ogidi da Nkpor, 6 kuma an kamasu ne tsakanin Awka da Amansea, Vanguard ta wallafa.

Sannan an kama 5 a datsin Onitsha da Nkpor, 7 a Oba da Nnewi, 6 a Nsugbe da Nkwelle-Ezunaka, 8 a Ogbunike da Abagana, 4 a Nawfia sai kuma 4 tsakanin Nimo da Abagana.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel