Da duminsa: APC ta yi babban rashi a jihar Delta, tsohon gwamna ya koma PDP

Da duminsa: APC ta yi babban rashi a jihar Delta, tsohon gwamna ya koma PDP

- Tsohon gwamnan jihar Delta a ranar Litinin zai sauya sheka daga APC zuwa jam'iyyar PDP

- Emmanuel Uduaghan, a cewar majiya mai tushe, zai koma PDP ne tare da dumbin magoya bayansa

- A jam'iyyar PDP ne Uduaghan ya ci zaben gwamnan Delta, inda ya yi shugabanci na shekaru 8, kafin daga bisani ya koma APC

Rahotannin da Legit.ng Hausa ke samu yanzu, na nuni da cewa tsohon gwamnan jihar Delta a ranar Litinin zai sauya sheka daga APC zuwa jam'iyyar PDP.

TVC News ta ruwaito cewar, tsohon gwamnan jihar, Emmanuel Uduaghan, a cewar majiya mai tushe, zai koma PDP ne tare da dumbin magoya bayansa.

Ana sa ran, tsohon gwamnan zai jagoranci dubunnan magoya bayansa zuwa jam'iyyar PDP, a rumfar zabensa da ke gunduma ta 5, Abigborodo, karamar hukumar Warri ta Arewa, da ke jihar.

KARANTA WANNAN: Elrufai ya magantu kan karɓar sunaye daga masu zaɓen sarkin Zazzau

Da duminsa: APC ta yi babban rashi a jihar Delta, tsohon gwamna ya koma PDP
Da duminsa: APC ta yi babban rashi a jihar Delta, tsohon gwamna ya koma PDP - tvcnewsng
Asali: Twitter

Rahotanni sun tabbatar da cewa tuni dai tsohon gwamnan ya gama shirye shiryen komawa PDP, jam'iyyar da aka zabe shi har ya yi gwamna na tsawon shekaru takwas a Delta.

Duk da cewa, Uduaghan bai tabbatar ba ko kuma karyata labarin komawarsa PDP ba, sai dai tuni wasu daga magoya bayansa, kamar Godwin Abigor, suka koma PDP makon da ya gabata.

KARANTA WANNAN: Gwamnatin Nigeria ta samu umurnin dakatar da yajin aikin NLC daga kotu

Godwin Abigor, ya kasance tsohon dan majalisar dokoki na jihar Delta, kuma na gaba gaba a magoya bayan tsohon gwamnan jihar, Uduaghan.

A wani labarin, Gwamnatin Nigeria ta samu sabon umurni daga kotu, na dakatar da kungiyar kwadago ta NLC da TUC daga shiga yajin aikin da suka shirya shiga ranar Litinin, 28 ga watan Satumba 2020.

Mai shari'a Ibrahim Galadima na kotun masana'antu ta kasa, ya bayar da umurnin a Abuja, biyo bayan bukatar hakan da Antoji Janar na kasa ya gabatar gaban kotun.

Galadima ya bayar da irin wannan umurnin na dakatarwa ga kungiyar jakadun zaman lafiya da hadin kai, a ranar Alhamis.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel