Tirkashi: Mutane sun yiwa Donald Trump ihun bama yi a lokacin da suka je jana'iza

Tirkashi: Mutane sun yiwa Donald Trump ihun bama yi a lokacin da suka je jana'iza

- Mutane sunyi wa shugaban kasa Donald Trump da matarsa ihun "bama so" a kotun koli ranar Alhamis

- Yanzu haka Donald da matarsa sun daina shiga jama'a saboda gudun wulakanci a cikin kasar Amurka

- Mai shari'ar kotun koli tace kada a maye gurbin ta da kowa har sai anyi sabon shugaban kasa, Donald ya musanta hakan

Mutane sunyi wa shugaban kasa Donald Trump da matarsa Melania Trump ihun "bama so! " yayin da suka je jana'izar mai shari'a Ruth Bader Ginsburg a kotun koli ranar Alhamis.

Sun kuma ta fadin "abi wasiyyar ta," suna tuno wasiyyar Ginsburg da tayi wa jikarta a kan koda ta mutu kada a maye gurbin ta da kowa har sai an kara zaben wani shugaban kasa.

Shugaban kasar ya karyata wasiyyar Ginsburg, inda yace ya tabbata yan jam'iyyar adawa ne suka kirkiro wasiyyar.

Shugaban kasa Donald Trump ya sha ihu, in da al'umma ke mishi ihun "Bama so" yayin da shi da matarsa suka je jana'izar mai shari'a Ruth Bader Ginsburg a kotun koli da safiyar Alhamis.

Shugaban kasa Donald da matarsa sun tsaya ne kusa da akwatin gawar Ginsburg, suna rike da tutar Amurka, yayin da sauran mutane ke kan matattakalar ginin kotun, wasu kuma suna bayan gine-ginen dake gefen kotun suna mishi ihun.

Yanzu haka, shugaban kasar da matarsa basa iya shiga cikin mutane saboda tsoron wulakanci irin wanda suka fuskanta a ranar Alhamis.

Jama'ar sun cigaba da ihu suna cewa "abi wasiyyar ta" suna tunatar da wasiyyar Ginsburg da tayi ranar Juma'ar da ta gabata cewa, kada a maye gurbin ta da kowa har sai an sake zaben wani shugaban kasar.

A yadda NPR suka bada rahoto, tsohuwar mai shekaru 87 a duniya ta ce wa jikarta, Clara Spera, "kada a maye gurbin ta da kowa har sai an sake zaben wani shugaban kasa, wannan itace wasiyyata ta karshe"

Shugaban kasar yayi watsi da wannan wasiyyar ta Ginsburg, inda ya ce yana zargin yan adawarsa a siyasa irinsu Sanata Chuck Schumer, yar majalisa Nancy Pelosi da Adam Schiff ne suka kirkira wannan wasiyya.

KU KARANTA: Yadda 'yan kungiyar asiri suka makantar da ni saboda na ki shiga kungiyarsu - Matashi

Tirkashi: Mutane sun yiwa Donald Trump ihun bama yi a lokacin da yaje kamfen
Tirkashi: Mutane sun yiwa Donald Trump ihun bama yi a lokacin da yaje kamfen. Hoto daga @Businessinsider
Source: Twitter

KU KARANTA: Borno: An rasa rayuka 3 a sabon harin 'yan ta'addan Boko Haram

"Wannan magana tayi kama da fitar iska, tayi dadi a baki. Amma tayi kama da maganar Schumer, ko Pelosi ko kuma Shifty Schiff," a cewar Trump kamar yadda Fox News suka ruwaito a farkon makonnan.

Tun a ranar Juma'a dubbannin jama'a ke zuwa kotun koli yin ta'aziyyar adalar mai shari'ar.

Duk da ba'a zaben alkali ana saura shekara daya zabe, gwamnati na kokarin maye gurbin Ginsburg da wani alkali mai adalci, ana tsara yadda za'a zabi alkali kafin ranar zaben shugaban kasa tazo.

Shugaban kasa Donald Trump yace zai fadi sunan alkalin da ya fitar ranar Asabar da yamma.

A wani labari na daban, wata 'yar Najeriya mai suna Hauwa Ojeifo ta samu gagarumar kyauta ta musamman daga gidauniyar Bill Gates da Melinda Gates ta shekarar 2020.

Kasancewar budurwar mai rajin kare hakkin jinsi da nakasassu ce, tana jagorantar wata kungiya mai taimako da bada shawarwari ga masu fama da rashin lafiyar kwakwalwa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Tags:
Online view pixel