Labarin ƙarya ne: Elrufai ya magantu kan karɓar sunaye daga masu zaɓen sarkin Zazzau

Labarin ƙarya ne: Elrufai ya magantu kan karɓar sunaye daga masu zaɓen sarkin Zazzau

- Gwamna Nasir Elrufai na jihar Kaduna ya karyata labarin da ake yadawa na cewar ya karbi sunaye daga masu zaben sarkin daga masarautar Zazzau

- Gwamnan ya ce a halin yanzu, kwamishinan harkokin masarautu da masu zaben sarki na nazari da tantance sunayen mutane 11 ne

- A cewarsa, sai bayan sun kammala tantancewar ne, shi kuma zai ce ga wanda zai zama Sarkin Zazzau na gaba, In Sha Allah

Gwamnan jihar Kaduna, Nasiru Elrufai ya musanta labarin da ake yadawa a kafafen watsa labarai na cewar ya karbi sunaye daga masu zaben sarkin Zazzau.

A cewar gwamnan, wannan labarin kanzon kurege ne kawai, kasancewar har yanzu, babu wani suna da ya zo gabansa, da sunan tantancewa don nada sabon sarki.

KARANTA WANNAN: Gwamnatin Nigeria ta samu umurnin dakatar da yajin aikin NLC daga kotu

Labarin karya ne: Elrufai ya magantu kan karbar sunaye daga masu zaben sarkin Zazzau
Labarin karya ne: Elrufai ya magantu kan karbar sunaye daga masu zaben sarkin Zazzau
Asali: Twitter

A sanarwar da ya fitar ta shafinsa na Twitter @elfurai a ranar Juma'a, gwamnan ya ce kwamishinan masarautu na nazarin sunaye 11, kuma masu zaben sarkin zasu tantance su.

Elrufai ya ce, zai duba cancantar wanda zai zama sarkin Zazzau ne kawai idan kwamishinan da masu zaben sarkin suka kammala tantance mutane 11, shi kuma sai ya ce ga sarki na gaba.

KARANTA WANNAN: Za a rufe tasoshin jiragen sama ranar Litinin, za su shiga yajin aiki

Sanarwar na cewa: "Kuyi hattara da labarin karya! Elrufai bai karbi komai ba. Kwamishinan harkokin masarautu na nazarin sunayen mutane bakwai, masu zaben sarki za su tantance.

"Daga karshe ne, ni kuma zan ce ga wanda zai zama sarkin Zazzau na gaba, In Sha Allah."

Idan ba ku manta ba, mun ruwaito maku labari daga jaridar Daily Trust, da ke cewa, masu zaben sarki a masarautar Zazzau sun gabatar da sunayen mutane uku ga gwamnan jihar Kaduna.

Ga sunayensu:

Alhaji Bashir Aminu, Iyan Zazzau Ya samu maki 89,

Alhaji Muhammed Munnir Jafaru, Yariman Zazzau, ya samu maki 87, da

Alhaji Aminu Shehu Idris, Turakin Karamin Zazzau ya samu maki 53 .

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel