Da duminsa: Gwamnatin Nigeria ta samu umurnin dakatar da yajin aikin NLC daga kotu

Da duminsa: Gwamnatin Nigeria ta samu umurnin dakatar da yajin aikin NLC daga kotu

- Gwamnatin tarayya ta samu umurnin dakatar da yajin aikin NLC da TUC daga kotun masana'antu ta kasa

- Kungiyoyin kwadago na NLC da TUC, sun sha alwashin shiga yajin aiki a ranar Litinin, 28 ga watan Satumba 2020 saboda karin kudin fetur da lantarki

- A hannu daya, kungiyoyin sufurin jiragen sama, suma sun ba mambobinsu umurnin shiga yajin aiki a ranar Litinin, lamarin da zai jawo rufe tashoshin jiragen sama na kasar

Gwamnatin Nigeria ta samu sabon umurni daga kotu, na dakatar da kungiyar kwadago ta NLC da TUC daga shiga yajin aikin da suka shirya shiga ranar Litinin, 28 ga watan Satumba 2020.

Mai shari'a Ibrahim Galadima na kotun masana'antu ta kasa, ya bayar da umurnin a Abuja, biyo bayan bukatar hakan da Antoji Janar na kasa ya gabatar gaban kotun.

KARANTA WANNAN: Za a rufe tasoshin jiragen sama ranar Litinin, za su shiga yajin aiki

Da duminsa: Gwamnatin Nigeria ta samu umurnin dakatar da yajin aikin NLC daga kotu
Da duminsa: Gwamnatin Nigeria ta samu umurnin dakatar da yajin aikin NLC daga kotu
Asali: Twitter

Galadima ya bayar da irin wannan umurnin na dakatarwa ga kungiyar jakadun zaman lafiya da hadin kai, a ranar Alhamis.

Kungiyoyin NLC da TUC sun sha alwashin shiga yajin aiki a ranar Litinin, sakamakon karin kudin man fetur da wutar lantarki da gwamnatin ta yi.

KARANTA WANNAN: Jihar Bauchi ta tsayar da ranar bude makarantu a cikin watan Oktoba

Kafin yanke hukuncin shiga yajin aikin, kungiyoyin kwadagon, sun bukaci gwamnati ta janye wannan karin kudade da ta yi, sai dai gwamnatin ba ta amsa wannan bukata ba.

A cewar kungiyar kwadago, karin kudin fetur da lantarki a dai dai wannan lokaci, ba ai karawa yan Nigeria komai ba sai bakar azaba da tsadar rayuwa.

A wani labari, kungiyoyin sufurin jiragen sama guda hudu, za su bi sahun kungiyar kwadago ta kasa NLC, shiga yajin aiki a ranar Litinin.

A cikin wata sanarwa a ranar Juma'a, kungiyoyin sun bukaci ma'aikatansu a sufurin jiragen sama da su yi zamansu a gida daga ranar Litinin, 28 ga watan Satumba.

Hakan na nufin cewa, za a rufe tashoshin jiragen sama a ranar Litinin.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel