Da duminsa: Bayern Munich ta lashe gasar cin kofin UEFA

Da duminsa: Bayern Munich ta lashe gasar cin kofin UEFA

- Kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munich ta lashe gasar cin kofin zakarun nahiyar turai, bayan lallasa Sevilla da cin 2-1

- Lucas Ocampos, dan wasan Sevilla ne ya fara zura kwallo a mintuna 13 na take wasan, sai dai Leon Goretzka da Javi Henandez sun mayar da martani

- Munich ta samu wannan nasarar ne karkashin mai horas da 'yan wasa Hansi Flick, a filin wasanni na Budapest

Kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munich ta samu nasarar lashe gasar cin kofin zakarun nahiyar turai 'UEFA Super Cup', bayan lallasa Sevilla da ci 2-1 a filin wasan Budapest.

Lucas Ocampos ya fara zurawa Sevilla kwallo a ragar Bayern Munich, bayan samun bugun daga kai sai mai tsaron raga ana mintuna 13 da take wasan.

KARANTA WANNAN: Sabbin mutane 125 sun kamu da cutar COVID-19, jimilla 57,849

Da duminsa: Bayern Munich ta lashe gasar cin kofin UEFA
Da duminsa: Bayern Munich ta lashe gasar cin kofin UEFA @vanguardngrnews
Source: Twitter

Sai dai Bayern Munich, sun mayar da martani ana mintuna 34, inda Leon Goretzka ya zura kwallo a ragar Sevilla.

A mintuna na 104 ne Javi Henandez ya samu nasarar zura kwallo ta biyu, inda ya baiwa kungiyar kwallon kafar Munich nasarar lashe gasar cin kofin UEFA.

KARANTA WANNAN: Buhari ya amince har yanzu Boko Haram da ƴan bindiga na cin kasuwarsu a Nigeria

Munich ta samu wannan nasarar ne karkashin mai horas da 'yan wasa Hansi Flick, wasan farko da aka fara bugawa da masu kallo a tsai tsaye tun bayan dawo da harkokin wasannin bayan annobar COVID-19.

Daga kasar Vietnam kuwa, rundunar 'yan sandan kasar ta cafke akalla kororon roba 324,000, wadanda aka riga da aka yi amfani da su, yanzu kuma ake sake gyarasu domin mayar da su kasuwa.

Rundunar 'yan sandan ta cafke buhunan kororon robar a wani gida mai lamba DX12, unguwar Hoa Nhut, gundumar Tan Vinh Hiep, yankin Binh Duong, da ke Kudancin Vietman.

A cewar jami'an rundunar, aikin mutanen gidan shine wankewa, busarwa da kuma gyara girman kororon robar, ta hanyar amfani da katago mai suffar mazakuta, kafin a shigar da su kasuwa.

Rahotanni sun bayyana cewa ana sayar da su ne a otel otel da gidajen karuwai, da ke kusa da gidan, inda kuma ake shigar da su sassa daban daban na kasar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel