Za mu gina sabuwar Najeriya: Lai Mohammed ya yi bayanin shagalin cikar Najeriya shekaru 60

Za mu gina sabuwar Najeriya: Lai Mohammed ya yi bayanin shagalin cikar Najeriya shekaru 60

- Ministan yada labarai da al'adu na Najeriya, Alhaji Lai Mohammed, ya bayyana yadda za su samar da sabuwar Najeriya

- Ministan yada labaran ya ce duk da kalubalen da ake fuskanta a kasar nan, samuwar sabuwar Najeriya karkashin Buhari ta cancanci murna

- Ya kara bayyana cewa, za a yi shagalin murnar amma ba gagarumi ba saboda annobar korona da ta zama ruwan dare

Lai Mohammed, ministan yada labarai da al'adu, ya ce mulkin kasar nan karkashin shugaban kasa Muhammadu Buhari, na kokarin saka kasar nan a hanyar da ta dace.

A yayin jawabi ga manema labarai a ranar Alhamis domin bayyana shirye-shiryen shagalin bikin cikar Najeriya shekaru 60, Mohammed ya ce tun bayan samun 'yancin kasar, an fuskanci yakin basasa, rikicin siyasa da kuma rashin tsaro.

Ministan ya ce wannan mulkin ya zo da sabon cigaba. "Wasu za su iya fara tunanin me yasa Najeriya za ta yi wannan shagalin bikin, ganin cewa akwai manyan kalubale da kasar ke fuskanta," yace.

"Hakazalika, a wasu al'adu, ana kallon shekaru 60 a matsayin tushen rayuwa kuma hakan yasa ake bikinta. Ga Najeriya, mulkin shugaba Buhari shine tushen cigaba.

“Gwamnatinsa na aiki tukuru wurin tabbatar da samuwar sabuwar Najeriya, saka tushen cigaba da fasaha ta hanyar samar da kayayyakin more rayuwa da suka hada da wutar lantarki, tituna, gada da layikan dogo da sauransu.

“Mulkin na karawa da yakar rashawa, rashin tsaro da kuma fadada hanyar tabbatar da tattalin arziki ta hanyar noma da kiwo tare da hako ma'adanai da sauransu," yace.

Ministan ya tabbatar da cewa, shagalin cikar Najeriya shekaru 60 za a yi ba tare da gagarumin taro ba, The Cable ta wallafa.

"Hakan yana da alaka da annobar korona da ta gallabi duniya, wacce ta sa kowacce kasa take kokarin dakile yaduwar cutar. Hakan yasa za a rasa wasu daga cikin shagulgulan murnar," yace.

KU KARANTA: Ambaliyar ruwa ta lashe rayuka 25, mutum 20 sun raunata

Za mu gina sabuwar Najeriya: Lai Mohammed ya yi bayanin shagalin cikar Najeriya shekaru 60
Za mu gina sabuwar Najeriya: Lai Mohammed ya yi bayanin shagalin cikar Najeriya shekaru 60. Hoto daga @Thecable
Asali: Twitter

KU KARANTA: 'Yan daba sun tare matar aure, sun yi awon gaba da takin da take tafe da shi

Idan za mu tuna, a tun farko watan Satumban shekarar nan ne gwamnatin tarayya ta bukaci masu hazakar kirkire-kirkire da zane, da su kawo zane wanda za a yi amfani da shi a yayin da kasar ke cika shekaru 60 da samun 'yancin kai.

A kowacce shekara, ranar 1 ga watan Oktoba kasar Najeriya ke shagalin bikin zagayowar ranar samun 'yancinta.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel