Nasarun Minallah: Sojoji sun kwato sama da mutane 20 daga 'yan bindiga a Katsina

Nasarun Minallah: Sojoji sun kwato sama da mutane 20 daga 'yan bindiga a Katsina

- Rundunar sojin Nigeria, ta bayyana cewa, ta samu nasarar kwato sama da mutane 20 daga hannun 'yan bindiga a sassa daban daban na jihar Katsina

- Haka zalika, dakarun atisayen THUNDER STRIKE, sun kashe yan bindiga da dama tare da lalata maboyarsu a dajin Kwaimbana, jihar Kaduna

- Daga shiyyar Arewa maso Gabas kuwa, dakarun atisayen LAFIYA DOLE sun kakkabe yan ta'adda da sansanoninsu a jihohin Borno, Yobe, Taraba da Adamawa

Sama da mutane 20 da aka yi garkuwa da su, da suka hada da mata 11 da kananun yaran da ba a san iyakarsu ba, suka samu ceto daga hannun 'yan bindiga, a sassa daban na jihar Katsina.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa, a garin Fankama da Sabon Layi, karamar hukumar Faskari, mutane 8 ne rundunar soji ta ceto su daga 'yan bindigar, bayan samun rahotanni.

Haka zalika, rundunar soji da ke atisayen 'Sahel Sanity' sun shiga rangadi a yankin Chabas, inda suka ceto direba da mata 11 da kananan yara, da aka sacesu a kan hanyar kasuwar Batsari.

KARANTA WANNAN: Buhari ya amince har yanzu Boko Haram da ƴan bindiga na cin kasuwarsu a Nigeria

Nasarun Minallah: Sojoji sun kwato sama da mutane 20 daga 'yan bindiga a Katsina
Nasarun Minallah: Sojoji sun kwato sama da mutane 20 daga 'yan bindiga a Katsina @HumAngle
Source: UGC

Kodinetan watsa labarai na rundunar sojin, Manjo Janar John Enenche, ya bayyana hakan a taron manema labarai na karshen mako, kan nasarorin da rundunar sojin ta samu.

A cewar MG John Enenche, "A shiyyar Arewa maso Yamma, dakarun atisayen HADARIN DAJI sun ci gaba da matsin lamba ga 'yan bindigar shiyyar, da ma dakile sauran ayyukan ta'addanci."

KARANTA WANNAN: Zaben Edo: Amurka ta magantu kan nasarar Obaseki

Ya kara da cewa, "A 'yan tsakanin nan, dakarun da aka tura sansanin Dansadau sun cafke wani dan bindiga kan hanyarsa ta zuwa kauyen Dandalla a Dansadau, Maru, jihar Zamfara.

"Haka zalika, Sashen rundunar sojin sama da ke atisayen THUNDER STRIKE sun kashe yan bindiga da dama da lalata maboyarsu a dajin Kwaimbana, jihar Kaduna."

"Sannan, rundunar sojin ta cafke masu safarar makamai 2 dauke da harsasai 1,620 masu tsayin 7.6mm a tsaunin Kudaru, hanyar Kaduna-Jos, karamar hukumar Lere, jihar Kaduna.

"A ranar 18 ga watan Satumbar 2020, dakarun da ke a sansanin BURUKUSUMA, sun kashe 'yan bindiga 7 a kauyen Magira, jihar Zamfara.

"A ranar 19 ga wannan watan, dakarun atisayen HADARIN DAJI tare da wasu 'yan sa kai, sun cafke yan bindiga 2 dauke da N1,300,000 a kauyen Baworaje, Talata Mafara, jihar Zamfara."

A wani ci gaban daga shiyyar Arewa maso Gabas, Eneche ya bayyana cewa, "A cikin wannan lokacin, dakarun atisayen LAFIYA DOLE sun kakkabe yan ta'adda da sansanoninsu a jihohin Borno, Yobe, Taraba da Adamawa.

"A tsakanin 17 da 20 na watan Satumba 2020, dakarun atisayen SAFE HAVEN sun kai sumama mabuyar 'yan SARA SUKA a garin Jenta Adamu, Rikkos da Gangaren Yan Doya, karamar hukumar Jos ta Arewa, jihar Filata.

"A yayin sumamen, an cafke wadanda ake zargi mutum 14, yayin da 12 ke dauke da wukake, 4 da adduna, wayoyin hannu guda 4, takubba 2, da kayan tsafe tsafe da kuma miyagun kwayoyi."

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya shaidawa Majalisar Dinkin Duniya cewa har yanzu mayakan Boko Haram da 'yan bindiga na cin karensu ba babbaka a cikin kasar.

Buhari ya sanar da hakan a ranar Laraba, yayin gabatar da jawabi a madadin kasar Nigeria, ta hanyar sakon bidiyo, a ranar farko na taron majalisar MDD karo na 75.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel