Daga ƙarshe: Buhari ya amince har yanzu Boko Haram da ƴan bindiga na cin kasuwarsu a Nigeria

Daga ƙarshe: Buhari ya amince har yanzu Boko Haram da ƴan bindiga na cin kasuwarsu a Nigeria

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gasgata cewa har yanzu mayakan Boko Haram da 'yan bindiga na ci gaba da cin karensu ba babbaka a Nigeria

- Buhari ya bayyana hakan ne ga Majalisar Dinkin Duniya, inda ya roki majalisar da sauran kasashe, da su hada karfi, don kawo karshen ta'addanci

- Shugaban kasar ya kuma tabbatar da cewa Nigeria za ta hada kai da WHO don samar da rikagafi da kayayyakin kariya daga COVID-19 don rabawa makarantu

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya shaidawa Majalisar Dinkin Duniya cewa har yanzu mayakan Boko Haram da 'yan bindiga na cin karensu ba babbaka a cikin kasar.

Buhari ya sanar da hakan a ranar Laraba, yayin gabatar da jawabi a madadin kasar Nigeria, ta hanyar sakon bidiyo, a ranar farko na taron majalisar MDD karo na 75.

Taken taron MDD karo na 75 shine: "Makomar Da Muke So, Majalisar Dinkin Duniya Da Muke So: Kara karfafa hadin guiwarmu wajen yakar annobar Coronavirus ta hanyar daukar matakai."

KARANTA WANNAN: Zaben Edo: Amurka ta magantu kan nasarar Obaseki

Daga ƙarshe: Buhari ya amince har yanzu Boko Haram da ƴan bindiga na cin kasuwarsu a Nigeria
Daga ƙarshe: Buhari ya amince har yanzu Boko Haram da ƴan bindiga na cin kasuwarsu a Nigeria - NGRPresident
Source: Twitter

Ya bukaci shuwagabannin duniya da su hada karfi da karfe wajen kawo karshen matsalar tsaro, yana mai nuni da cewa haren haren da 'yan bindiga ke kaiwa kasashen duniya, ya fara yin yawa.

Ya ce Nigeria na ci gaba da sa tsammanin gudunmawa daga MDD a bangaren hadin guiwa don kawo karshen 'yan ta'adda, da kuma kasashen da ke makwaftaka da ita, kamar Chadi da Kamaru.

KARANTA WANNAN: Daliban kwalejin KPS 5, da mutane 18 sun mutu a fashewar tankar fetur a Kogi

Shugaban kasar ya kara da cewa Nigeria za ta ci gaba da bunkasa rayuwar al'umma, gine gine da kuma mayar da wadanda ta'addancin ya dai-daita zuwa muhallansu.

Buhari ya ce, gwamnatinsa za ta cimma hakan ne ta hanyar amfani da hukumar bunkasa shiyyar Arewa Maso Gabas da gwamnatin ta samar a shekarun da suka gabata.

Cinikayyar makamai a bakar kasuwa.

Buhari ya ce Nigeria na ci gaba da damuwa kan yadda ake cinikayyar manya da kananan makamai a bakaken kasuwanni, musamman a Africa.

Ya jaddada kokarin Nigeria na tabbatar da kammala aikin Tafkin Chadi, inda ya yi kira ga sauran kasashen ketare da su taimaka don tara $50bn da za a kammala aikin.

Shirin matakan kariya da tsafta ga Makarantu

Ya sanar da cewa Nigeria ce za ta bakunci taron Bada Kariya ga Makarantu na duniya karo na 4, da za a gudanar a shekarar 2021.

Ya bayyana cewa Nigeria za ta hada kai da hukumar lafiya ta duniya (WHO) da wasu kasashe wajen samar da rigakafi da matakan kariya na cutar COVID-19 ga makarantu.

A wani labarin, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince a fitar da $1.96bn don gina layin dogo da ya tashi daga Kano-Jigawa-Katsina-Jibia zuwa Maradi a Jamhuriyar Nijar.

Shugaba Buhari, ya amince da fitar da kudaden ne a ranar Laraba, a yayin zaman majalisar zartaswa ta kasa (FEC) a fadar shugaban kasa, Abuja.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel