Sabon rahoto: Daliban kwalejin KPS 5, da mutane 18 sun mutu a fashewar tankar fetur a Kogi

Sabon rahoto: Daliban kwalejin KPS 5, da mutane 18 sun mutu a fashewar tankar fetur a Kogi

- Tankar man fetur mallakin kamfanin NNPC ta yi hatsari, inda ta kama da wuta nan take, a Felele da ke kan hanyar Lokoja-Abuja, jihar Kogi

- Sakamakon wannan mummunan hatsari, dalibai 5, kananan yara guda 3, da kuma wasu mutane 15 suka kone kurmus a nan take

- Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya bayyana kaduwarsa na faruwar wannan hatsari, tare da rokon daliban kwalejin KSP da su kwantar da hankulansu

Dalibai biyar daga kwalejin Kogi (KSP) Lokoja, da kananan yara uku, tare da wasu mutane 15 suka mutu a ranar Laraba, sakamakon fashewar tankar man fetur a Lokoja, jihar Kogi.

Jaridar Tribune Online ta ruwaito cewa tankar man ta afkawa wasu motocin a Felele da ke hanyar Lokoja-Abuja, da misalin karfe 8:30am, yayin da wasu motocin ke fada mata.

Tankar man fetur din mallakar kamfanin NNPC, ana hasashen burkinta ya tsinke, inda ta fadawa motici 5, mashina 2 da kekuna 3, yayin ta kashe mutane 23 bayan ta kama da wuta.

KARANTA WANNAN: Buhari ya nada Abba Tijjani a matsayin sabon shugaban NCMM

Yanzu-yanzu: Tankar man fetur ta fashe, mutane 10 sun mutu nan take a Kogi
Yanzu-yanzu: Tankar man fetur ta fashe, mutane 10 sun mutu nan take a Kogi
Asali: Twitter

Wadanda hatsarin ya rutsa da su akwai daliban kwalejin jihar guda 5, kananan yara 'yan makarantar Nazire guda 3, sai mutane 15, inda suka kone kurmus.

Akwai kuma Mr Samson, da matarsa tare da yaransa guda uku, daga cikin mutanen da suka kone a cikin wutar, rahotanni sun nuna cewa yana hanyarsa ta kai yaransa makaranta.

Wasu da lamarin ya faru akan idanunsu, sun bayyana cewa, direban tankar, ya yi kokarin shawo kan motar bayan tsunkewar burkin, amma hakan ya ci tura.

KARANTA WANNAN: Buhari ya nada Abba Tijjani a matsayin sabon shugaban NCMM

Yanzu-yanzu: Tankar man fetur ta fashe, mutane 10 sun mutu nan take a Kogi
Yanzu-yanzu: Tankar man fetur ta fashe, mutane 10 sun mutu nan take a Kogi
Asali: Twitter

Direban tankar, a cewar mutane, ya yi amfani da hannunsa tare da gargadar mutanen da ke kan hanyar da su kauce, amma ga wasu, lokaci ya kure masu, ya afka kansu.

Tuni dai, hukumar kashe gobara ta yan kwana kwana da kuma jami'an kiyaye hadurra suka kai dauki, domin ceto mutane da kuma kashe wutar.

Kwamandan FRSC na sashen, Idris Fika Ali ya ce akalla mutane 23 ne suka mutu a fashewar tankar, yayin da wani yaro ya tsira da ransa da raunuka.

Yanzu-yanzu: Tankar man fetur ta fashe, mutane 10 sun mutu nan take a Kogi
Yanzu-yanzu: Tankar man fetur ta fashe, mutane 10 sun mutu nan take a Kogi
Asali: Twitter

Gwamna Yahaya Bello ya bayyana kaduwarsa kan fashewar tankar man.

Gwamnan a cikin wata sanarwa daga Sakataren watsa labaransa, Onogwu Mohammed, ya bayyana jimaminsa akan rasuwar mutanen da asarar dukiyoyi.

Ya kuma bukaci daliban kwalejin jihar da su kwantar da hankulansu.

Yanzu-yanzu: Tankar man fetur ta fashe, mutane 10 sun mutu nan take a Kogi
Yanzu-yanzu: Tankar man fetur ta fashe, mutane 10 sun mutu nan take a Kogi
Asali: Twitter

A wani labarin, An nada Farfesa Abba Isa Tijjani a matsayin sabon shugaban hukumar gidajen ajiye kayan tarihi ta kasa (NCMM).

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya amince da nadin Tijjani a matsayin sabon shugaban NCMM, wanda ya daga darajar masanin ilimukan daga Malami zuwa Shugaba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel