Da duminsa: Buhari ya nada Abba Tijjani a matsayin sabon shugaban NCMM

Da duminsa: Buhari ya nada Abba Tijjani a matsayin sabon shugaban NCMM

- An sake yin nadin wani sabon mukami mai muhimmanci a wata hukumar gwamnatin tarayya

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada Abba Tijjani a matsayin sabon shugaban hukumar NCMM

- Kasancewar masani mai zurfin ilimi a fannoni daban daban, Tijjani Farfesa ne a kimiyyar gidajen ajiye kayan tarihi da kuma nazarin rayuwar dan adam a jami'ar UNIMAID

An nada Farfesa Abba Isa Tijjani a matsayin sabon shugaban hukumar gidajen ajiye kayan tarihi ta kasa (NCMM)

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya amince da nadin Tijjani a matsayin sabon shugaban NCMM, wanda ya daga darajar masanin ilimuka daga Malami zuwa Shugaba.

KARANTA WANNAN: Wadatar da kasa da abinci: Buhari ya zabtare farashin taki a Nigeria

Da duminsa: Buhari ya nada Abba Tijjani a matsayin sabon shugaban NCMM
Da duminsa: Buhari ya nada Abba Tijjani a matsayin sabon shugaban NCMM
Asali: Twitter

Kasancewar Farfesa a kimiyyar gidajen ajiye kayan tarihi da kuma nazarin rayuwar dan adam daga jami'ar Maiduguri, shi ne shugaban sashen fasahar kirkirar zane zane na jami'ar.

Haka zalika shine tsohon kodinetan shugaban sashen fasahar kirkire kirkire na hannu.

KARANTA WANNAN: Kasar Saudiya ta amince a ci gaba da yin Umrah, ta gindaya sharudda

Abbah, kafin samun wannan mukami na gwamnatin tarayya, ya rike mukamin daraktan cibiyar nazarin dorewar al'addun gargajiya (CSCS) na jami'ar Maiduguri.

Ya kuma kasance daraktan kwamiti kuma shugaban shirin N-DAAD, Makarantar dorewar muradun karni "Tabbatar da dorewar al'adu da ci gabansu a Yammacin Afrika."

An tabbatar da dacewar Tijjani a matsayin shugaban hukumar NCMM la'akari da kwarewa, gogewa da kuma tarin iliminsa a wannan fanni.

A wani labarin, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi jimamin mutuwar Sarakunan Borno guda biyu - Shehun Bama, Shehu Kyari Ibn Umar El-Kanemi da Sarkin Biu Mai Umar Mustapha Aliyu.

A cewarsa, mutuwar Sarakunan guda biyu a lokaci daya, duka biyu ne mai wuyar shanyewa, kuma dole 'yan Nigeria su ji radadin mutuwar Sarakunan biyu.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa daga hadimin shugaban kasar ta fuskar watsa labarai, Garba Shehu da ya rabawa manena labarai a ranar Talata.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel