Mutuwar Sarakunan Borno guda biyu a lokaci daya ya girgiza ni - Buhari ya magantu

Mutuwar Sarakunan Borno guda biyu a lokaci daya ya girgiza ni - Buhari ya magantu

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mika sakon ta'aziyyar rasuwar Sarkin Shehun Bama da Sarkin Biu

- A cewar shugaban kasar, mutuwar Sarakunan a kusan lokaci daya, duka biyu ne mai wuyar shanyewa

- Haka zalika, ya jinjinawa gwamnan Borno, Babagana Umara Zulum, bisa namijin kokarinsa, na sadaukar da rayuwarsa ga ceton rayukan al'ummar sa

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi jimamin mutuwar Sarakunan Borno guda biyu - Shehun Bama, Shehu Kyari Ibn Umar El-Kanemi da Sarkin Biu Mai Umar Mustapha Aliyu.

A cewarsa, mutuwar Sarakunan guda biyu a lokaci daya, duka biyu ne mai wuyar shanyewa, kuma dole 'yan Nigeria su ji radadin mutuwar Sarakunan biyu.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa daga hadimin shugaban kasar ta fuskar watsa labarai, Garba Shehu da ya rabawa manena labarai a ranar Talata.

KARANTA WANNAN: Mijina yana amfani da dadironsa domin ci mun mutunci - Matar aure ta kokawa kotu

Mutuwar Sarakunan Borno guda biyu a lokaci daya ya girgiza ni - Buhari ya magantu
Mutuwar Sarakunan Borno guda biyu a lokaci daya ya girgiza ni - Buhari ya magantu
Source: Twitter

A cikin wasiku da ya aikawa masarautun biyu, bisa jagorancin Gwamna Babagana Zulum da kuma Shehun Borno, Shehu Abubakar Ibn-Umar Garbai El-Kanemi.

A cikin wasikun da suka samu rakiyar tawaga daga fadar shugaban kasa, bisa jagorancin Malam Adamu, Ministan Ilimi, Buhari ya ce: "Irin wannan mutuwar, dole ta jijjiga kowa."

KARANTA WANNAN: Shugaban Buhari ya saka labule da Gwamnan Kwara a 'Aso Rock' (Hotuna)

Buhari ya yi nuni da cewa "Gudunmowarsu wajen wanzar da zaman lafiya a masarautunsu musamman a shekarun ta'addancin Boko Haram, abun tunawa da yaba masu ne.

"Hakika, yadda suka nuna jajurcewa, zai zama abun buga misali ga wadanda za su gaje su, kuma, ba za a taba mantawa da dumbin ci gaban da suka kawowa masarautunsu ba."

Shugaban tawagar ya jinjinawa Gwamna Babagana Zulum na fuskantar hatsararruka daban daban domin wanzar da zaman lafiya da tsare rayukan al'ummar jiharsa.

Gwamnan ya bukaci tawagar, da ta hada da Ministoci guda biyu, Mustapha Shehuri, Noma da raya karkara da kum Injiniya Abubakar Aliyu, ayyuka da gidaje, da kuma Garba Shehu, da su isar da godiyar al'umar Borno ga shugaban kasa akan taimakon da ya ke yiwa jihar.

Rahotannin da Legit.ng Hausa ta samu na nuni da cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gana da gwamnan jihar Kwara, Abdulrahman Abdulrazaq.

Shugaban kasar ya gana da gwamnan ne a fadar shugaban kasa Abuja, a ranar Talata, 22 ga watan Satumba 2020, kamar yadda hadiminsa Buhari Sallau ya wallafa a Twitter.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel