Yanzu yanzu: Shugaban Buhari ya saka labule da Gwamnan Kwara a 'Aso Rock' (Hotuna)

Yanzu yanzu: Shugaban Buhari ya saka labule da Gwamnan Kwara a 'Aso Rock' (Hotuna)

Rahotannin da Legit.ng Hausa ta samu yanzu na nuni da cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya shiga ganawa da gwamnan jihar Kwara, Abdulrahman Abdulrazaq.

Shugaban kasar ya gana da gwamnan ne a fadar shugaban kasa Abuja, a ranar Talata, 22 ga watan Satumba 2020, kamar yadda hadiminsa Buhari Sallau ya wallafa a Twitter.

KARANTA WANNAN: Daukar mutane 774,000 aiki daga jihohi 36: Muhimmin bayani daga FG

Sai dai har zuwa yanzu, ba a bayyana dalilin zuwan gwamnan jihar Kwara fadar shugaban kasar ba, ko sanin abunda aka tattauna yayin ganawar.

Cikakken labarin yana zuwa.

Ga hotunan ganawar:

Yanzu yanzu: Shugaban Buhari ya saka labule Gwamnan Kwara a 'Aso Rock' (Hotuna)
Yanzu yanzu: Shugaban Buhari ya saka labule Gwamnan Kwara a 'Aso Rock' (Hotuna)
Source: Twitter

KARANTA WANNAN: Mijina yana amfani da dadironsa domin ci mun mutunci - Matar aure ta kokawa kotu

Yanzu yanzu: Shugaban Buhari ya saka labule Gwamnan Kwara a 'Aso Rock' (Hotuna)
Yanzu yanzu: Shugaban Buhari ya saka labule Gwamnan Kwara a 'Aso Rock' (Hotuna)
Source: Twitter

A wani labarin, Rahotanni sun bayyana cewa aski ya zo gaban goshi, a yayin da ake daukar mutane 774,000 a karkashin shirin gwamnatin tarayya na 'Special Public Works (SPW)'

Sai dai, har zuwa yanzu, wasu jihohin ba su samu damar kammala daukar ma'aikatan da aka basu dama ba, wanda ya sa aka kara masu wa'adin mako daya.

Ministan kwadago da daukar aiki na cikin gida, Festus Keyamo ya ce har yanzu ranar 1 ga watan Oktoba ita ce ranar da za a fara shirin. Daukar mutane 774,000 aiki daga jihohi 36.

Ya zuwa ranar Litinin da ta zamo ranar karshe ta daukar aikin, jihohin Yobe da Ebonyi sun aika da sunayen wadanda za su ci gajiyar shirin.

A ranar Litinin, Keyamo ya ce, "Mun gudanar da taron hukumar daukar aiki ta kasa NDE, inda muka duba yiyuwar kara wasu kwanaki, don jihohi su aiko da sunayen mutanen su.

"Har yanzu muna fatan fara shirin a ranar 1 ga watan Oktoba. A yanzu dai muna fuskantar wasu matsalolin cikin gida, amma zamu magance su kafin lokacin...

"A mako mai zuwa ne zamu sanar da wakilanmu da zasu kaddamar da shirin a jihohinsu. Kuma bankuna 6 ne za a yi amfani dasu don tura kudi ga masu cin gajiyar shirin," cewar Keyamo.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel