Diyar Osinbajo ta haihu, ya samu jikansa na farko a duniya

Diyar Osinbajo ta haihu, ya samu jikansa na farko a duniya

- Mataimakin shugaban kasar Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo, ya bayyana labari mai matukar dadi a shafinsa na Twitter

- Dan siyasar ya sanar da karuwar da iyalansa suka samu bayan diyarsa, Oludamilola ta haifa jikansu na farko

- Kakan mai cike da annashuwa tare da nishadi, ya sanar da cewa diyarsa ta haifa yaro namiji kuma ya zama kaka

Mataimakin shugaban kasar Najeriya, Yemi Osinbajo, ya yi wallafa labari mai dadi a shafinsa na Twitter don ya sanar da masoyansa cewa ya zama kaka.

Dan siyasar ya bayyana cewa, daya daga cikin 'ya'yansa mata da mijinta sun haifa yaro namiji.

Osinbajo ya ce, diyarsa mai suna Oludamilola da mijinta mai suna Oluseun sun haifa santalelen yaro namiji.

Dan siyasar ya mika godiyarsa ga Ubangiji a yayin da yake sanar da duniya cewa ya zama kaka.

KU KARANTA: Saurayi ya kashe budurwarsa bayan an bashi N2m domin amfani da ita wurin tsaf

Diyar Osinbajo ta haihu, ya samu jikansa na farko a duniya
Diyar Osinbajo ta haihu, ya samu jikansa na farko a duniya
Source: Instagram

KU KARANTA: Bayan ya yiwa saurayin kanwarsa dukan tsiya, saurayin ya siyo mata sabuwar mota mai tsadar gaske a matsayin godiya

A wani labari na daban, a ranar Juma'a, 4 ga watan Satumban 2020 aka daura auren Aisha Hanan Buhari, autar shugaban kasar Najeriya, da Muhammad Turad Sha'aban, mai bai wa ministan ayyuka shawara na musamman, Babatunde Fashola.

An yi gagarumin daurin auren a fadar shugaban kasa Muhammadu Buhari da ke Aso Villa a Abuja.

Sakamakon annobar korona da ta zama ruwan dare, tun a katin gayyatar an bayyana cewa ba za a yi bikin cike da taro ba domin biyayya ga dokokin hukumar dakile yaduwar cututtuka.

Cike da farin ciki tare da mika godiya ga masoya, 'yan uwa da abokan arziki, uwargidan shugaban kasa, Aisha Buhari, ta wallafa bidiyon yadda aka daura auren da kuma hotunan shagalin bikin.

Kamar yadda ta wallafa a shafinta na Instagram, ta ce "A yau babbar rana ce ta farin ciki ga iyalaina a yayin da muka shaida auren diyata Aisha Hanan Buhari da Muhammad Turad Sani Sha'aban.

"Ina matukar farin ciki da sakonnin fatan alheri da kuma goyon baya daga iyalaina, abokai da masoya.

"Bari in yi amfani da wannan damar wurin mika sakon godiya ga wadanda suka samu damar halarta da wadandan basu samu dama ba.

"Sakamakon fahimtar wannan lokaci na tsananin annobar duniya da muka yi da kuma bukatar kiyaye shawarwarin masana kiwon lafiyarmu na karanta taro.

"Muna godiya a kan addu'o'inku ga ma'auratan a yayin da suka shiga sabuwar rayuwar aure."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Tags:
Online view pixel