Yadda aka kama dan shekara 16 da bindiga a makarantar sakandare

Yadda aka kama dan shekara 16 da bindiga a makarantar sakandare

- Yan sandan jihar Anambra sun kama wani saurayi mai shekaru 16 da haihuwa wanda ake zargi da zama dan kungiyar asiri

- Saurayin yaje da bindiga makarantar su ta sakandare dake unguwar Igboukwu a karamar hukumar Aguaata a jihar

- Yan sandan sunce dama suna irin wannan kamen saboda damkar masu laifuka kamar yan kungiyar asiri a karshen kowacce shekara

Kakakin rundunar yan sandan jihar Anambra, Muhammad Haruna, yace suna irin wannan kamen saboda damkar masu laifi musamman na kungiyar asiri a wuraren da ake zargin maboyarsu ne.

Yace an kama mutane 15 da ake zargi a tsakanin Ogidi da Nkpor, 6 kuma an kamasu ne tsakanin Awka da Amansea, Vanguard ta wallafa.

Sannan an kama 5 a datsin Onitsha da Nkpor, 7 a Oba da Nnewi, 6 a Nsugbe da Nkwelle-Ezunaka, 8 a Ogbunike da Abagana, 4 a Nawfia sai kuma 4 tsakanin Nimo da Abagana.

Sauran 12 a wuraren Ifitedunu da Awkuzu, 4 a Amikwo, 5 a Nsugbe da 3-3 sai kuma 4 a Ebenebe da Ugbenu.

Kamar yadda kakakin yan sandan yace, antura 40 daga cikinsu kotu, sai kuma 15 da aka tantancesu kuma aka sakesu.

KU KARANTA: Bayan ya yiwa saurayin kanwarsa dukan tsiya, saurayin ya siyo mata sabuwar mota mai tsadar gaske a matsayin godiya

Yadda aka kama dan shekara 16 da bindiga a makarantar sakandare
Yadda aka kama dan shekara 16 da bindiga a makarantar sakandare. Hoto daga Vanguard
Source: UGC

KU KARANTA: Yadda wani karamin yaro dan Najeriya ya kera jirgin sama wanda yake tashi

Ya kara da cewa, 5 daga cikin wadanda ake zargin suna hannun yan sanda saboda karancin shekarunsu, 20 kuma sun tabbatar da cewa su yan kungiyar asiri ne da bakinsu.

Abubuwan da aka karba a hannayensu sun hada da bindigogi guda biyu, fate-fate guda 10, adduna 5, daga 2, bindigogi guda biyu da sauran miyagun makamai.

Kwamishinan yan sanda na jihar, Mr John Abang, ya tabbatar wa mutanen jihar Anambra cewa zai kula da lafiyarsu da dukiyoyinsu.

A wani labari na daban, wasu 'yan bindiga da ake zargin mayakan Boko Haram ne sun kai wa wasu kauyuka biyu hari a garin Borno inda suka kashe a kalla mutum uku tare da raunata wasu.

Jaridar Sahara Reporters ta gano cewa, 'yan ta'addan sun kai hari kauyukan Gareri da Kuwami da ke karamar hukumar Magumeri ta jihar Borno.

Magumeri karamar hukuma ce da ke arewacin Borno, kuma tana da nisan kusan kilomita 40 daga Maiduguri, babban birnin jihar, inda ake fuskantar hare-hare.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel