Zaben Edo: Jami'in tattara zabe na karamar hukumar Orhionmwon ya yi batan dabo

Zaben Edo: Jami'in tattara zabe na karamar hukumar Orhionmwon ya yi batan dabo

- Rahotanni sun bayyana cewa jami'in da ke tattara zaben karamar hukumar Orhionmwon, jihar Edo ya yi batan dabo

- Da farko an hangi jami'in a cibiyar tattara sakamakon zaben, amma daga bisani aka nema sa aka rasa

- Batan dabon jami'in tattara zaben, ya jawo shakku a tsakanin jam'iyyun siyasar, inda wakilansu ke ganin cewa akwai lauje cikin nadi

Rahotannin da Legit.ng Hausa ke samu na nuni da cewa jami'in da ke tattara zaben karamar hukumar Orhionmwon, jihar Edo ya yi batan dabo.

Kamar yadda BBC ta ruwaito, hukumar INEC ce ta fara bayyana fargabarta na rashin sanin inda jami'in nata ya ke, a lokacin da ake tattara sakamakon zaben gwamnan jihar.

Da farko, wani jami'in PDP ne ya hankaltar da mutane kan batan jami'in, sai dai wani jami'in APC ya karyata zarginsa, yana mai cewa PDP na son ta yi magudin zabe ne kawai.

Kamar yadda BBC ta ruwaito, an tabbatar da ganin jami'in hukumar ta INEC a cibiyar tattara sakamakon zaben, sai dai, an neme sa an rasa daga baya.

KARANTA WANNAN: Muhimman abubuwa 5 da suka faru a ranar da aka gudanar da zaben Edo

Zaben Edo: Jami'in tattara zabe na karamar hukumar Orhionmwon ya yi batan dabo
Zaben Edo: Jami'in tattara zabe na karamar hukumar Orhionmwon ya yi batan dabo
Source: Original

Hukumar zabe mai zaman kanta INEC a cewar jaridar Sahara Reporters, ta tabbatar da batan jami'in nata, tana mai cewa jami'in ya bata ne jim kadan bayan zuwansa cibiyar.

A wani labarin, Jam'iyyar PDP ta sha gaban jam'iyyar APC a yayin da hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) ke cigaba da sakin sakamakon zaben kujerar gwamnan jihar Edo.

Hakan na nufin cewa dan takarar jam'iyyar PDP kuma gwamnan jihar Edo mai ci, Godwin Obaseki, ya na kan gaba da rinjaye mai yawa a yayin da ake cigaba da sakin sakamakon zaben.

KARANTA WANNAN: Kidayar Kuri'u: PDP ta sha gaban APC da banbancin kuri'a fiye da dubu 50

Ga wasu daga cikin sakamakon zaben kamar yadda INEC ta saki;

Karamar hukumar Igueben PDP: 7,870 APC: 5,199

Karamar hukumar Esan central PDP: 10,964 APC: 6,719

Karamar hukumar Esan north-east PDP: 13,579 APC: 6,559

Karamar hukumar Esan south-east PDP: 10,565 APC: 9,237

Karamar hukumar Ikpoba Okha PDP: 41,030 APC: 18,218

Karamar hukumar Owan east PDP: 14,762 APC: 19,295

Karamar hukumar Etsako west PDP 17,959 APC 26,140

Karamar hukumar Egor PDP: 27, 621 APC: 10, 202

Karamar hukumar Esan west PDP – 17,433 APC – 7,189

Karamar hukumar Uhunmwonde PDP: 10,022 APC: 5,972

Jimilla: PDP: 171,805 APC: 114,730

Tazarar da ke tsakanin PDP da APC a halin yanzu: 57,075

Ana ci gaba da tattarawa tare da sanar da sakamakon zabe daga sauran kananan hukumomi 8.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Online view pixel