Da duminsa: Sanwo-Olu ya bayar da umurnin bude gaba daya Masallatai da Majami'un Lagos

Da duminsa: Sanwo-Olu ya bayar da umurnin bude gaba daya Masallatai da Majami'un Lagos

- Gwamnatin jihar Lagos, ta bayar da umurnin bude Masallatai da Majami'un jihar, hakan zai basu damar gudanar da ibadu a kowacce rana

- Idan ba a manta ba, sakamakon annobar COVID-19, gwamnatin jihar ta sahalewa Masallatai da Majami'u budewa a ranakun Juma'a da Lahadi kawai

- Haka zalika, Gwamna Sanwo-Olu ya amice a bude gidajen kallo da kuma gidajen motsa jiki amma da sharadin ba da tazara da wanke hannu

Gwamnan jihar Lagos, Babajide Sanwo-Olu a ranar Lahadi, ya bayar da umurnin bude gaba daya majami'u da masallatan jihar, hakan zai basu damar gudanar da ibada ba dokantawa.

Ibadun da wuraren bautar za su rinka gabatarwa yanzu ya hada da ibadun karshen mako, da na kowacce rana, kamar yadda suka saba kafin zuwan COVID-19.

Kafin bayar da wannan umurni, an amincewa majami'u budewa ne a ranakun Lahadi kawai, yayin da aka amince Masallatai su bude a ranakun Juma'a kawai.

KARANTA WANNAN: Kidayar Kuri'u: PDP ta sha gaban APC da banbancin kuri'a fiye da dubu 50

Da duminsa: Sanwo-Olu ya bayar da umurnin bude gaba daya Masallatai da Majami'un Lagos
Da duminsa: Sanwo-Olu ya bayar da umurnin bude gaba daya Masallatai da Majami'un Lagos
Source: Depositphotos

Sai dai Gwamnan a ranar Asabar ya ce a yanzu Masallatai da majami'u za su iya dawo da ibadunsu kamar yadda suka saba yi a baya.

"Dangane da wuraren ibadunmu, yanzu mun amince Masallatai su dawo da yin Salloli sau biyar a rana; yayin da majami'u, su dawo da yin ibadunsu na tsakiyar mako da karshen mako.

"Kada mu manta da cewa har yanzu annobar COVID-19 na tare da mu, ya zama wajibi mu dauki matakan kariya musamman ga kananan yaranmu, malamai, iyaye da al'uma baki daya.

"Gaba daya wadannan matakan kariyan da tsare tsare, alhaki ne ga masu ruwa da tsaki na addinai su tabbatar an kiyaye su," a cewar Sanwo-Olu.

KARANTA WANNAN: Bidiyo: Rundunar yan sanda ta fara farautar jami'inta da aka nuna yana shan shisha

Ya kara da cewa daga yanzu, an amincewa wuraren kallo da motsa jiki su bude, amma da sharadin daukar kashi 33 na mutanen da suka saba dauka, barin kujeru biyu a tsakani.

Ga wuraren motsa jiki kuwa, ya zama wajibi a rinka tsaftace karafuna da sauran kayan motsa jiki da ake amfani da su, don kare yaduwar cutar.

A cewar gwamnan, "a wata mai zuwa, Oktoba, za mu sanar da matsayarmu kan bude sauran bangarorin tattalin arziki: Gidajen rawar dare, gidajen mashaya, gidajen biki, tashoshin mota."

A wani labarin, Rundunar 'yan sanda ta fara bincike kan wani bidiyo da ya karade yanar gizo da ke nuna wani mutumi sanye da kakin rundunar yana shan shisha.

Rundunar a shafinta na Twitter, a ranar Lahadi ta bayyana cewa ta mika bidiyon ga sashen kwararru don gano gaskiyar bidiyon, da kuma sanin mutumin.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel