Soja da ke yakar Boko Haram ya kashe kansa, ya bar wa matarsa wasika mai ratsa zuciya

Soja da ke yakar Boko Haram ya kashe kansa, ya bar wa matarsa wasika mai ratsa zuciya

- Mummunan labarin da ke zuwa a yau shine labarin wani soja mai mukamin lance corporal daga jihar Yobe

- Wata majiya daga rundunarsa ta ce ya daga bindiga inda ya saita kansa a ranar Alhamis ya sakarwa kansa harsashi

- Sojan da ya kashe kansa a bakin aiki, ya bar wa matarsa wasika amma har yanzu ba a san dalilinsa na kashe kansa ba

Wani soja da ke yakar Boko Haram a yankin arewa maso gabas ta Najeriya ya kashe kansa, The Cable ta ruwaito.

Majiyoyi sun sanar da cewa, sojan mai mukamin lance corporal da ke aikinsa a Buni Gari da ke karamar hukumar Gujba ta jihar Yobe, ya kashe kansa a ranar Alhamis yayin da yake bakin aiki.

Har yanzu dai ba a san dalilinsa na kashe kansa ba, amma majiyoyin sun ce ya dauka bindigarsa inda ya saita kansa tare da sakin kunamar.

"Ya harba kansa a kai, kuma a take ya mutu kafin sauran sojojin su kawo masa dauki," wata majiya daga rundunar sojin ta sanar.

An gano cewa, sojan ya bar wa matarsa wata wasika.

An dauke gawarsa zuwa asibiti, kuma majiyar ta ce a halin yanzu ana binciken al'amarin.

Mai magana da yawun rundunar, Sagir Musa, har yanzu ba a samesa ba balle a ji ta bakinsa a kan lamarin.

Sannanen abu ne idan aka ce sojojin da ke karkashin rundunar Operation Lafiya Dole da ke yankin arewa maso gabas, suna korafi a kan karancin walwala.

KU KARANTA: Jerin sunaye: Jihohi 15 da za su amfana da tallafin bayan korona - NEC

Soja da ke yakar Boko Haram ya kashe kansa, ya bar wa matarsa wasika mai ratsa zuciya
Soja da ke yakar Boko Haram ya kashe kansa, ya bar wa matarsa wasika mai ratsa zuciya. Hoto daga The Cable
Source: UGC

KU KARANTA: Dantabawa, makusancin Yari, ya yi magana a kan zarginsa da ake da taron sirri da 'yan bindiga

A wani labari na daban, mun samu wani labari mai ban takaici daga Jaridar Cable cewa wani karamin Sojan kasar nan ya harbi mai gidan sa wanda yake Kyaftin a Garin Banki a cikin Jihar Borno a Ranar wata Lahadin da kimanin karfe 9:13 na dare.

Wani kurtun Soja ya harbe mai gidan sa a Borno Yanzu haka majiyar ta Jaridar The Cable tace an wuce da Sojan zuwa asibitin Sojoji da ke yankin.

Shi kuma wannan Soja da yayi wannan tabargaza yana tsare a hannun manyan sa bayan an karbe kayan bindigar da ke hannun sa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel