Jerin sunaye: Jihohi 15 da za su amfana da tallafin bayan korona - NEC

Jerin sunaye: Jihohi 15 da za su amfana da tallafin bayan korona - NEC

- Kwamitin tattalin arziki na Najeriya, ya ce an zaba wasu jihohi 15 da za su amfana daga tallafin bayan korona a bangaren ilimi

- Jihohin sune Abia, Anambra, Akwa Ibom, Benue, Ebonyi, Jigawa, Kaduna, Katsina da sauran wasu bakwai

- Wadannan jihohin an zabesu ne bayan cike wasu sharudda biyu cikin uku da aka gindaya na karbar tallafin

Kwamitin tattalin arziki na kasar (NEC), ta ce jihohin kasar nan 15 ne za su amfana da tallafin ilimi a matsayon tallafin bayan annobar korona.

Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya bayyana hakan a tattaunawar da yayi da manema labaran gidan gwamnati ta yanar gizo bayan taron NEC da aka yi, wanda Farfesa Yemi Osinbajo ya jagoranta a ranar Alhamis.

An shugabanci taron ta yanar gizo ta fadar shugaban kasa da ke babban birnin tarayya da ke Abuja, Solacebase ta wallafa.

"Ina farin cikin sanar da cewa gwamnatin tarayya ta fitar da tsarikan tallafin kudi domin taimaka wa jihohi a bangaren ilimi bayan korona.

"Zababbun jihohin da za su amfana da tallafin ilimi na korona sune wadannan: Abia, Anambra, Akwa Ibom, Benue, Ebonyi, Jigawa, Kaduna, Katsina, Kebbi, Kano, Nassarawa, Niger, Plateau, Sokoto da Zamfara.

"Wadannan sune jihohin da suka cike sharadi biyu daga cikin uku na karbar tallafin wanda bankin duniya da wasu suka assasa," yace.

KU KARANTA: Mutumin da yake acaba yana biyawa kanshi kudin makaranta ya zama dalibin da yafi kowa sakamako mai kyau

Jerin sunaye: Jihohi 15 da za su amfana da tallafin bayan korona - NEC
Jerin sunaye: Jihohi 15 da za su amfana da tallafin bayan korona - NEC. Hoto daga Solacebase
Source: Twitter

KU KARANTA: Yadda wani biri ya saci wayar wani mutumi yaje ya dinga daukar hoto da bidiyo da ita

A wani labari na daban, mun ji cewa gwamnatin jihar Kano ta ce ta ware fiye da Naira miliyan 800 da nufin gyara makarantun boko na gwamnati da ke jihar.

Mai girma gwamna Abdullahi Umar Ganduje zai kashe wadannan makudan kudi ne domin ganin an dawo da darajar makarantun gwamnati a jihar.

Gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje za ta batar da Naira miliyan 20 a kowace karamar hukuma, adadin jimillar abin da za a kashe shi ne Miliyan 880.

Za a zabi makaranta guda ne a kowace karamar hukuma kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta bayyana.

An fitar da wannan rahoto ne a ranar Lahadi. Kwamishinan ilmi na jihar Kano, Sanusi Kiru ya yi wannan bayani a lokacin da ya zanta da ‘yan Najeriya bayan an kaddamar da wannan shiri a jiya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Online view pixel