COVID-19: FG ta sanar da lokacin da za a samu rigakafi

COVID-19: FG ta sanar da lokacin da za a samu rigakafi

- Gwamnatin tarayya ta sanar da cewa babu yuwuwar samun rigakafin cutar korona a wanann shekarar

- Ministan lafiya, Osagie Ehanire, ya ce dole ne 'yan Najeriya su kiyaye dokokin yaduwar cutar domin za a bude dukkan kasuwanci da harkokin kasar

- Ministan ya kara da yin amfani da wannan damar wurin kira ga ma'aikatan lafiya da su ajiye yajin aikin da suka fada

Gwamnatin tarayya ta ja kunnen 'yan Najeriya akan su kiyaye yayin wannan annobar cutar korona, ta kara da cewa rigakafi ba zai sami ba har sai shekarar 2021.

A yayin jawabi yayin tattaunawar kwamitin fadar shugaban kasa a kan cutar korona a ranar Alhamis a garin Abuja, ministan lafiya, Osagie Rhanire, ya bukaci 'yan Najeriya da su kiyaye da dukkan dokokin dakile yaduwar cutar.

"Rigakafi ba zai samu ba sai a shekara mai zuwa. Babu wai tabbataccen magani da aka tabbatar da cewa yana maganin cutar, amma dole ne mu bude dukkan abubuwan da muka rufe a kasar nan," yace.

Ya yi kira ga 'yan Najeriya da su kiyaye dokokin dakile annobar korona domin hana yaduwarta a kasar nan.

Kiyaye dukkan dokokin hana yaduwar cutar kamar saka takunkumin fuska, nesa-nesa da juna, daina yin taruka da sauransu, za su taka babbar rawar gani wurin dakile cutar.

A yayin bayanin, ministan ya kara da rokon ma'aikatan lafiya da su gaggauta dawowa daga yajin aikin da suka tsunduma.

Kamar yadda yace, hanyar shawo kan matsala shine tattaunawa da gwamnatin tarayyar ba bore ba.

"Ina yin amfani da wannan damar wurin kara kira ga kungiyar ma'aikatan lafiya da su duba majinyata su dawo daga yajin aikin da suka fada a yayin da muke tattaunawa da su.

“Akwai matukar muhimmanci idan muka tunatar da kanmu cewa cutar korona da gaske akwai ta, kuma a hankali take yaduwa a wasu sassan duniya.

"Akwai matukar hatsari idan mutum ya yadda cewa tana tafiya ne cutar ganin yadda yawan masu cutar ke raguwa. Wasu kasashe suna fuskantar tashin cutar a karo na biyu kuma tana sake yaduwa," yace.

KU KARANTA: Yadda wani biri ya saci wayar wani mutumi yaje ya dinga daukar hoto da bidiyo da ita

COVID-19: FG ta sanar da lokacin da za a samu rigakafi
COVID-19: FG ta sanar da lokacin da za a samu rigakafi. Hoto daga Channels TV
Source: Twitter

KU KARANTA: Mutumin da yake acaba yana biyawa kanshi kudin makaranta ya zama dalibin da yafi kowa sakamako mai kyau

A wani labari na daban, hukumar hana Yaduwar Cututtuka ta Najeriya wato NCDC ta bayyana cewa an sallami mutane 3442 dake fama da cutar Korona a birnin tarayya Abuja, jihar Kwara da wasu jihohin Najeriya a yau kadai.

Hakan na kunshe ne a cikin sanarwar da hukumar NCDC ta fitar da misalin karfe 11:30 na daren ranar Laraba 16 ga Satumba, shekarar 2020. Hukumar ta ce annobar cutar Covid-19 ta sake harbin sabbin mutane 126 a fadin Najeriya.

Jawabin hukumar yace: "Warakan da muka samu yau mutane 2,967 a birnin tarayya da 103 a jihar Kwara da aka yiwa jinya cikin gida bisa sharrudan da hukumar ta gindaya."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel