Da duminsa: FG ta fitar da muhimmiyar sanarwa ga masu amfani da bankuna

Da duminsa: FG ta fitar da muhimmiyar sanarwa ga masu amfani da bankuna

- FG ta bukaci dukkanin masu amfani da asusun ajiye kudi na banki, da su tabbata sun karbi takardun cike bayanan kai-da-kai 'Self-Certification Forms'

- Gwamnatin ta bukaci masu asusun ajiyar kudi a bankuna daban daban, da su karbi takardun, su cike, su mayarwa kowanne banki

- Gaza cike wadannan takardu da mayar da su ga bankunan, zai jawo hukunci da ya kama daga cin tara ko garkame asusun mutum

Gwamnatin tarayya ta yi kira ga daukacin 'yan Nigeria masu asusun ajiye kudade a bankuna ko kamfanonin inshora da su gaggauta karbar takardun cike bayanan kai 'Self-Certification Forms'.

A cewar sanarwar da gwamnatin tarayyar ta fitar ta shafinta na Twitter a ranar Alhamis, ta ce bayan cike takardun, a mayar da su ga bankuna ko kamfanonin ajiye kudaden.

Ga wadanda ke amfani asusun ajiye kudin a bankuna daban daban, sanarwar ta ce dole ya cikewa kowanne banki wadannan takardu, ya mayar da takardun ga kowanne banki.

KARANTA WANNAN: Batanci ga Allah: Gwamnatin Kano ta yi wa UNICEF martani kan shiga maganar Omar Farouk

Da duminsa: FG ta fitar da muhimmiyar sanarwa ga masu amfani da bankuna
Da duminsa: FG ta fitar da muhimmiyar sanarwa ga masu amfani da bankuna
Asali: Twitter

A cewar gwamnatin, bankuna na bukatar wadannan takardu domin yin amfani da su wajen aiwatar da tsare tsare na dokar kudaden shiga daga haraji, doka ta 2019.

Takardun da za a cike, kuma a mayar da su ga bankunan guda uku ne:

  • Takardar bayanin mamallaki (mutum daya), ko kamfani, ko kungiya, da ke da mallakar asusun banki
  • Takardar shaidar wakilci (Ga wadanda ke wakiltar mamallakin asusu, misalin amintacce ga mai asusun ko lauyansa, da sauransu)
  • Takardar cikakken bayanin mutum daya (mamallakin asusun bankin), kamar yadda bayanan suke a lokacin bude asusun bakin

KARANTA WANNAN: Ma'aikata sun garkame ofishin hukumar PCC, sun hana kowa shiga

Gwamnatin ta tabbatar da cewa, "ga duk wanda ya gaza cike wadannan takardu, to zai fuskanci hukunci da ya kama daga cin tara ko kuma garkame masa asusun bankinsa."

A karshe hukumar ta bukaci mutane, su tuntubi shafukan hukumar domin neman karin bayani, a shafin twitter @firsNigeria, sai kuma adireshin yanar gizo, http://firs.gov.ng.

A wani labarin, Majalisar zartarwa ta tarayya (FEC) ta amince da kafa wata hukuma da za ta kula da kadarorin da aka kwato daga hannun mabarnata da ma su yi wa tattalin arziki zagon kasa.

Ministan shari'a kuma babban lauyan gwamnatin tarayya, Abubakar Malami, ne ya sanar da hakan ga manema labarai.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel